Home Back

Leverkusen ta lashe gasar Bundesliga ta 2024

dw.com 2024/5/18
Bundesliga - Bayer Leverkusen vs SV Werder Bremen
Hoto: EPA/CHRISTOPHER NEUNDORF

Shekaru 120 bayan kafuwarta, Bayern Leverkusen ta tashe gasar Bundesliga a karon farko bayan lallasa kungiyar Bremen da ci 5 da nema a filin wasa na BayArena yayin da ya rage makonni hudu a karkare kakar wasannin ta bana.

Tawagar ta Leverkusen karkashin mai horas wa Xavi Alonzo ta kawo karshen tarihi na yaya babba Bayern München da ta shafe shekaru 12 tana jan zan zarenta a wannan a gasar tare da yi wa sauran kungiyoyi fintinkau.

Baya ga kwace goruba a hannun kuturu, babban tarihin da Bayenr Leverkusen ta kafa shi ne a kakar wannan shekara kungiyar ta buga wasanni 43 rigis a gasannin daban-daban da tare da yin rashin nasara ba, sannan ta bai wa kungiyar da ke biya mata a teburin Bundesliga tazarar maki 16.

A yanzu dai Leverkusen za ta mayar da hankali ne kan karamin kofin zakarun nahiyar Turai watau Europa League inda take neman kai wa mataki na kusa da na karshe bayan ta doke Westam Ham ta Ingila da ci 2 da nema a tsikiyar makon nan, da kuma wasan karshen na kofin kalu bale na Jamus da za ta buga a ranar 25 ga watan Mayu a birnin Berlin.

People are also reading