Home Back

Jirgin Ƙasan Kaduna Zuwa Kano Zai Fara Aiki Farkon 2025

leadership.ng 6 days ago
Jirgin Ƙasan Kaduna Zuwa Kano Zai Fara Aiki Farkon 2025 

Titin jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Kano zai fara aiki a farkon shekarar 2025, a cewar Fidet Okhiria, Manajan Daraktan Hukumar Jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC).

A yayin ziyarar da ya kai tashar jirgin ƙasa ta Rigasa da ke Kaduna, Okhiria ya shaida cewa titin jirgin ya isa ƙaramar hukumar Maƙarfi daga Kano. Ya tabbatar da samun  ƙalubale irin su tsadar dizal da rashin tsaro, waɗanda suka yi tasiri wajan sa aikin tafiya a sannu sannu.

Okhiria ya jaddada ƙoƙarin gwamnati na sanya farashi mai sauƙi ga sufurin jiragen ƙasa duk da ƙarin farashin dizal. Ya kuma bayyana matakan da gwamnatin tarayya ta ɗauka na inganta tsaro da suka haɗa da sanya ido kan hanyar jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna da kuma yiwuwar amfani da fasaha a nan gaba wajen lura da jiragen ƙasa da kuma hanyoyin da za a daƙile duk wata ɓarna.

Fidet Okhiria
Fidet Okhiria MD NRC

A kan batun tikiti, Okhiria ce gabatar da tikitin zamani (e-tikiti) ya rage yawan masu sojan gonar sayen tikiti da kuma rage cuɗanya tsakanin ma’aikata da matafiya.

People are also reading