Home Back

APC Ta Zargi Kwankwaso Da Shirya Wa Ganduje Maƙarƙashiya Kafin Zaben 2027

leadership.ng 2024/5/19
2023: Idan Ka Isa Ka Shirya Tattaki Irin Namu A Kano – Ganduje Ya Kalubalanci Kwankwaso 

Jam’iyyar APC ta zargi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, da yi wa shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje zagon kasa kafin zaben 2027. 

Mai bai wa APC shawara kan harkokin shari’a, Abdulkareem Kana ne, ya yi wannan zargin.

Ya bayyana haka ne yayin wata hira da ya yi a gidan talabijin na Channels a ranar Litinin, inda ya zargi shugabancin NNPP a Jihar Kano da kokarin raba Ganduje da mukaminsa.

Kana ya kara da cewa kokarin NNPP ba zai yi nasara ba na haifar da cikas a jam’iyyar APC.

“Wadannan ayyuka na da nufin tayar da hankalinmu, amma ba za su yi nasara ba.

“Na samu damar yin aiki da Ganduje, kuma na shaida sadaukarwarsa da jagorancinsa. Gogaggen dan siyasa ne wanda ya bai wa jam’iyyarmu gudunmawa.”

Da yake mayar da martani, sakataren yada labarai na jami’yyar NNPP na kasa, Ladipo Johnson, ya yi watsi da zargin, inda ya bayyana jam’iyyar APC a matsayin wadda ta fada cikin rudani.

Johnson ya bayyana cewa Kwankwaso ba shi da hannu a al’amuran jam’iyyar APC da Ganduje, inda ya ce shugaban na APC shi ne ya kunno wa kansa matsaloli tun tali-tali.

Johnson ya ce, “Matsalolin Ganduje sun samo asali ne daga ayyukansa, babu tasirin wani daga waje. A halin yanzu yana fuskantar tuhuma daga shugabannin mazabarsa kuma ba shi da kwarin gwiwar fuskantar tuhumar da ake yi masa a kotu.”

People are also reading