ƘAZAMAR SIYASAR ONDO: An bindige kodinetan kamfen ɗin Gwamna Aiyedatiwa na zaɓen fidda-gwanin APC
Kwanaki kaɗan bayan kammala zaɓen fidda-gwanin APC na ‘yan takarar gwamnan Jihar Ondo, an bindige wani jigo a cikin kodinetocin kamfen ɗin Gwamna Lucky Aiyedatiwa.
An bindige Alaba Abbey a ranar Asabar, kwanaki bayan kammala zaɓen fidda-gwanin, wanda wasu ‘yan takara suka shiga duk kuwa da ƙoƙarin hana su shiga takarar da wasu jiga-jigan APC suka yi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an bindige Abbey ranar Asabar, kuma ba a gane ko wane su ka yi amfani da bindiga suka kashe shi ɗin ba.
An kashe shi a gidan sadake Supare Akoko, cikin Ƙaramar Hukumar Akoko ta Kudu maso Yamma.
Mamacin ya kasance kafin rasuwar sa shi ne Kodinetan Kamfen ɗin Gwamna Aiyedatiwa, LACO-SF.
Kuma ya kasance Baturen Zaɓen Fidda-gwani na Mazaɓa ta 10, a ƙaramar sa.
Yayan sa mai suna Samuel Abbey ya ce an bindige shi a ƙofar gidan sa, wajen ƙarfe 9 na dare, a ranar Asabar, bayan ya dawo kenan gida.
LACO-SF ta yi tir da kisan, kuma ta yi kira ga jami’an tsaro su kare rayukan mambobin su.