Home Back

RUƊANIN SIYASAR KANO: Gwamna Abba ya gana da NSA Ribadu

premiumtimesng.com 2024/7/4
RUƊANIN SIYASAR KANO: Gwamna Abba ya gana da NSA Ribadu

Gwamna Abba Kabir-Yusif Yusuf ya gana da Mashawarcin Musamman kan Harkokin Tsaro na Shugaban Ƙasa, Nuhu Ribadu a ranar Alhamis, a Abuja.

Ba a dai san abin da suka tattauna ba, amma gwamnan ya ce sun yi “ganawa mai tasiri kuma mai armashi” da NSA ɗin.

Ganawar ta zo daidai lokacin da ake ruɗanin sarautar Kano, mako guda bayan cire Aminu Ado da kuma naɗa sabon Sarki Sanusi Lamiɗo Sanusi.

Idan ba a manta ba, Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam ya zargi Ribadu da shiga gaba wajen ƙoƙarin bi ta bayan gida a maida Aminu kan gadon mulki. Ribadu ya ƙaryata, kuma ya nemi afuwa, wadda mataimakin ya bayar ba tare da ɓata lokaci ba.

Tuni dai harkoki na tafiya daidai a fadar Sarki Muhammadu Sanusi II, inda hakimai da ƙungiyoyi daban-daban da shugabannin al’umma ke tururuwar zuwa yin gaisuwa da kuma mubaya’a.

People are also reading