Home Back

SHIRIN A YI TA TA ƘARE: Sojoji za su tura sabbin dakaru 5,937 domin kakkaɓe Boko Haram, ‘yan bindiga, tsagerun IPOB

premiumtimesng.com 2024/7/3
KISAN GILLAR SOJOJI 17 A DELTA: Yadda aka guntule kawunan soja 14, aka farke cikin su aka fizge zuciyar su

Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, Taoreed Lagbaja, ya bayyana cewa za a tura sabbin sojojin da aka ɗauka su 5,937 wuraren yaƙi da ‘yan bindiga, tsagerun IPOB da dukkan wasu yankunan ake fuskantar masu tayar da zaune tsaye.

Lagbaja ya bayyana haka a lokacin da ake faretin yaye kuratan sojoji kashi na 86, a Makarantar Yaje Kuratan Sojoji, daffo da ke Zariya, a ranar Asabar.

Lagbaja wanda shi ne babban baƙo na musamman, ya ƙara da cewa zaratan sabbin sojojin masu jini a jika za su kasance cikin shirin magance matsaloli da ƙalubalen tsaro da ke addabar ƙasar nan.

“Waɗannan sabbin sojoji da aka yaye a yau, za su shiga cikin shirin magance matsalolin tsaro a Arewa maso Gabas, yaƙi da ‘yan bindiga, masu satar shanu a Arewa maso Yamma.

“Za su yi yaƙi da rikice-rikicen makiyaya da manoma a Arewa ta Tsakiya, za su daƙile ƙumajin masu tayar da ƙayar bayan ƙoƙarin ɓallewa daga Najeriya, masu ƙungiyoyin asiri da masu lalata kadarorin gwamnati a Kudu maso Kudu da Kudu maso Yamma.” Inji Lagbaja.

Ya ce aikin horarwar da ake yi abu ne ba mai yankewa ba a ɓangaren sojoji, tare da yin nuni da cewa Rundunar Sojojin Najeriya ta kuma shirya masu wani ƙasaitaccen horo bayan wannan yayewa da aka yi masu, ta yadda za su ƙara samun ƙwarewa sosai ɓangaren sarrafa makamai da sauran kayan aikin sojoji.

Ya ce hakan zai sa su ƙware sosai wajen iya tunkara, fuskanta da juriya wajen kafsa ƙazamin yaƙi.

Da yake wa sabbin sojojin su 5,937 murnar kammala samun horaswa, Lagbaja ya ce ita rayuwar soja fa rayuwa ce ta sadaukar da rai ga ƙasa, ta hanyar kare ta, har ma ya sadaukar da ran sa domin kare ƙasar sa idan hakan ya zama tilas.

People are also reading