Home Back

Karin Kudin Wutar Lantarki Da Yadda Ya Girgiza Masu Amfani Da Manyan Layuka

leadership.ng 2024/5/10
Karin Kudin Wutar Lantarki Da Yadda Ya Girgiza Masu Amfani Da Manyan Layuka

Rukunin kwastomomin da ke amfani da wutar lantarki masu amfani da ajin farko wato Band ‘A’ a halin yanzu suna bukatar ware a kalla naira 170,000 domin biyan kudin lantarki a kowace wata guda, sabanin naira 50,000 da suke biya kafin yanzu.

Su dai abokan huldar kamfanonin lantarki da suke ajin Band ‘A’ su ne masu shan wutar lantarki na tsawon awanni 20 a kowace rana, inda a halin yanzu za su ke biyan naira 225 na kudin wutan da suka sha a kowace sa’a sabanin naira 66 da suke biya a da baya kafin yanzu.

Biyo bayan karin kudin wuta da kaso 240 da aka yi wa kwastomomin wutar lantarki ‘yan ajin farko band A farashin wutar da suke sha ya tashi daga naira 66 a kowace kilowatt sa’a daya (KwH) inda ya haura zuwa naira 225 a kowace sa’a da kuma matakin ya fara daga wannan watan.

Hukumar kula da wutar lantarki ta Nijeriya (NERC) a ranar Larabar da ta gabata ta amince da karin kudin wutar lantarki daga kan naira 66 a sa’a daya zuwa naira 225 a sa’a daya ga kamfanonin rarraba wutar lantarki da suke sassan Nijeriya (DisCos).

Mataimakin shugaban NERC, Musliu Oseni, shine ya shaida hakan a lokacin da ke ganawa da ‘yan jarida a Abuja, ya ce, karin kudin ya shafa rukunin ajin da suke samun wuta na awanni 20 ko fiye a kowace rana ne kawai a fadin kasar nan.  Sauran kwastomomin da suke kan ajin Bands B, C, D da kuma E wadanda suke shan wuta na kasa da awanni 20 a kowace rana su wannan karin bai shafa ba.

NERC ta kara da cewa kaso 15 na cikin dari na masu amfani da wutar lantarki da DisCos ke rabawa ne wannan karin zai shafa da suke matakin samun wuta na awa 20 kowace rana.

Oseni ya kara da cewa NERC ta bada umarnin a rage darajar wasu masu amfani da tsarin aji Band ‘A’ amma kuma ba su cika ka’idojin amfani da wuta na awanni 20 a kowace rana ba, zuwa azuzuwan da suke kasa daidai da kwazonsu.

“Muna da turaku (feeders) da ke shan wuta 800 da suke rukunin aji Band A, amma kuma yanzu za a rage su zuwa 500. Don haka, a halin yanzu kaso 17 cikin dari na masu shan wuta a matakin A ne kawai suka cancanci zama a ajin Band A.

“Hukumarmu ta yi amfani da fasaha wajen gano turakun zukan wuta da suke amsar wuta daga kamfanonin rarraba wutar lantarki a Nijeriya da a halin yanzu suke kan rukunin Band A amma kuma ba su cika ka’idojin kasancewa a wannan ajin ba, don haka su wadannan masu shan wutan an bada umarnin a rage matsayinsu cikin gaggawa zuwa azuzuwan da suke kasa,” ya shaida.

A cewarsa, bisa matakin tabbatar da an bi wannan umarnin, an umarci DisCos da su baza jami’ansu zuwa tarukan da aka umarci a saukesu daga masu morar wuta na awa 20 zuwa kasa domin tabbatar da an bi wannan umarnin kuma an aiwatar da hakan.

“Domin kuma tabbatar da cewa kwastomomi na samun huldar kai tsaye da DisCos. An umarcesu da su wallafa lambobin tuntuba na jami’an sunturi da tawagar karta-kwana ga kwastomomi domin suke samunsu a lokacin bukatun hakan.

“Rashin cike wani ka’ida daga masu shan wuta a rukunin Band A kan iya janyo kai tsaye a sauke kwastomomi daga matakin zuwa kasa,” ya shaida.

Oseni ya kara da cewa a duk lokacin da DisCo ya kasa cimma burin kwastomomi cikin kwanaki biyu, a rana ta uku da safe dole kamfanin ya wallafa cikakken bayani zuwa ga lambar wayar kwastomin da abun ya shafa.

“Dole su yi bayanin dalilin da ya sanya ba su iya gudanar da aikin cikin kwanaki biyu ba kuma su mika kwafin wannan bayanin ga hukuma,” ya kara shaidawa.

LEADERSHIP ta bada labarin cewa kungiyoyin kwadago da wasu mutane masu kishi da dama sun shawarci gwamnatin tarayya da kada ta biye wa shawarar asusun bada lamuni ta duniya (IMF) wajen cire tallafin wutar lantarki.

A rahoton baya-bayan nan da asusun bada bashi na duniya IMF ya fitar, ya ce, akwai bukatar gwamnatin Nijeriya ta kawar da dukkanin wasu tallafi da take bayarwa tare da karkatar da wannan rarar zuwa shirye-shiryen da za su kyautata walwala da jin dadin jama’an kasar.

Domin dakile matsin rayuwa da ake ciki, IMF ta bada shawarar cewa a tura kudaden tallafi zuwa asusun ‘yan Nijeriya da ke fama da fatara domin rage musu kaifin matsin da ake ciki.

LEADERSHIP ta labarto cewa gwamnatin tarayya ta kusa kammala dukkanin shirye-shiryen da suka shafi bada tallafin wuta. A yanzu haka gwamnatin tarayya ta rage tallafin da take bai wa sashin wuta da kaso 15 cikin 100.

Kan wannan tashin gauron zabin farashin lantarki, LEADERSHIP ta yi nazarin cewa kwastomomin da ke rukunin Band ‘A’ da suke cin gajiyar na’urar sanyaya abubuwa firiza, fankoki a kalla uku, na’urar sanyaya muhalli AC, gulof na hasken wuta da yawansu ya kai 15, abun goge kaya guda daya, abun dumama abinci da na dafa ruwan zafi, da suke neman naira dubu 50 a da baya domin biyan kudin wuta a kowace wata, yanzu kwastoma mai irin wannan burin na neman naira 170,000 domin biyan kudin wutan gidansa sakamakon karin kudin wuta da kaso 240.9.

Da ya ke nacewa kan karin, jami’in NERC ya ce, kwastomomin da ke brand A kada su damu da cewa za su ke biyan kudin wuta mai yawa, yanzu haka za su samu saukin amfani da gas ko fetur din jannarato saboda za su ke samun nagartaccen wuta na tsawon awa 20 a kowace rana wanda zai iye biya musu dukkanin bukatunsu na yau da gobe.

Oseni ya bada tabbacin cewa dukkanin wanda ke kan rukunin samun wuta na awa 20 a kowace rana daga wajen DisCos kuma sai ya kasance baya samun wutan da ya kai wannan adadin, kai tsaye na da cikakken ikon yin korafi kuma za a bi masa kadinsa.

Sannan, ya ce, kwastomomin da kamfanonin rarraba wutar lantarki suke kasa basu wutar awa 20 alhali suna ajin A, su ma za a sauke su daga kan layin A zuwa B kila ma C domin dacewa da abun da ya dace suke samu.

Wakilinmu ya labarto cewa Ajin A: Su na samun wuta na tsawon awa 20 a kullum; Ajin B: Suna samun wuta ta tsawon awa 16 a kullum; Ajin C: Suna samun wutar lantarki ta tsawon awa 12 a kullum; Ajin D: Suna samun wutar lantarki ta tsawon awa 8 a rana da kuma Ajin E: Suna samun wutar lantarki ta tsawon awa 4 a rana.

Abin da ya bayyana a fili yanzu shi ne cewa ba kowa da kowa cire tallafin zai shafa ba, masu amfani da wutar lantarki kashi 15 ne kawai, amma kuma su ne ke shan kashi 40% na wutar lantarki a Nijeriya matakin zai shafa.

Da suke suka kan sabon karin kudin lantarki, kungiyoyin kwadago da kwastomomin wutar lantarki sun yi tir da matakin gwamnatin tarayya na kara kudin wuta ga rukunin A fadin kasar nan.

Duk da akwai bayanan da ke cewa kamfanoni na shirin kaddamar da hanyar samun wutarsu na daban domin kauce wa wannan tsadar wutar lantarkin.

Yayin da kungiyar kwadago a Nijeriya (NLC) ta gargadi gwamnatin tarayya kan kara dulmiya ‘yan Nijeriya cikin matsin rayuwa da kunci da tsadar raywa da tsadar lantarki, musamman ga kamfanoni masu karamin karfi (SMEs), sun ce karin kudin lantarki zai kara jefa abubuwa cikin tsada ne kawai, duk kuwa da cewa tunin wasu kayayyaki da daman gaske suka yi tashin gwauron zabi a halin da ake ciki.

NLC ta kara da cewa karin kudin lantarki a irin wannan yanayin da kasar nan ke fama da matsin rayuwa kwata-kwata ba tunani ne mai kyau ba.

Kungiyar ta lura kan cewa a halin da ake ciki ‘yan Nijeriya na kokuwar yadda za su yi manejin rayuwarsu da tsadar kayan masarufi, tare da cewa, duk wata gwamnati ta kwarai ba za so kara jefasu cikin mawuyacin hali ba, muddin ba in ba ta dukufa neman mafita garesu ba, ba za ta tashi kara kudin wuta da kusan kaso 300 ba.

Mai rikon babban sakataren NLC na kasa Kwamared Ismail Bello, a ganawarsa da LEADERSHIP, ya nanata muhimmancin kiran da kungiyar nasu ta yi tun da farko na cewa a cefanar da bangaren kawai a huta.

Kwamared Bello sai ya yi kira ga gwamnati da ta sake tunani da zurfinn nazari wajen janye batun karin kudin lantarki, inda ya nusar da ita cewa tabbas hakan zai kara jefa al’umman Nijeriya cikin fatara da talauci ne.“

People are also reading