Home Back

Gwamnan Kano Ya Tallafa Wa Maniyyatan Jihar Da Kudin Guziri

leadership.ng 2024/6/26
Kano

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya umarci a fitar da naira miliyan 376 domin cike gibin da aka samu na guzurin alhazan (BTA) jihar sakamakon hauhawar farashin dala.

Wannan na faruwa ne saboda yadda farashin kudaden waje ya matukar shafar kudaden da alhazai suka biya a aikin hajin bana, wanda har an samu wadanda da suka fasa tafiyar sakamakon rashin isassun kudi.

Sanarwar haka ta fito ne daga darakta janar na watsa labarai a ofishin gwamnan, Sanusi Bature, ya kuma yi bayanin cewa, tun da farko hukumar Alhazai at Kasa (NAHCON) ta ayyana kudin guzuri a matsayin Dala 500 lokacin ana canza dala a Naira 1,200 a halin yanzu dalan ya kai Naira 1,500, abin da ya haifar da babbar gibi.

Sanarwa ta kuma kara da cewa, Gwamna Yusuf ya yi wa alhazan albishir din ne a yayin da yake jawabi a wajen taron bita da aka shirya wa alhazan a kan yadda ake gudanar da wasu ayyukan hajji, ya ce, wannan tallafin zai taimaka wajen cike gibin N121,000 da kowanne Alhaji zai samu.

A halin yanzu kuma gwamnan ya nada mataimakiinsa Kwamrade Aminu Abdulsalam a matsayin Amirul Hajj na bana, shi ne kuma zai jagoranci tawagar gwamnatin jihar a aikin hajjin bana, cikin aikinsa kuma akwai kula da jin dadin alhazai na abin da ya shafi abinci, wurin kwana, kula da lafiya da dai sauransu.

People are also reading