Home Back

Sin Tana Fatan Bayar Da Gudummawa Ga Inganta Mu’ammalar Wayewar Kai Da Ci Gaban Duniya

leadership.ng 2024/6/26
Sin Tana Fatan Bayar Da Gudummawa Ga Inganta Mu’ammalar Wayewar Kai Da Ci Gaban Duniya

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian, ya ce kudurin da aka zartas a babban taron MDD kwanan nan, mai nasaba da samar da “Ranar tattauna harkokin wayewar kai ta duniya” wanda Sin ta gabatar, ya nuna cewa ajandar raya wayewar kan duniya ta dace da bukatun zamani, kuma ra’ayoyi, da dabarun Sin suna samun karbuwa, da goyon baya, da amsa daga kasashe da dama. 

Lin Jian wanda ya bayyana hakan a Talatar nan, yayin da ya jagoranci taron manema labarai na rana rana da aka saba gudanarwa, ya ce Sin tana fatan yin aiki tare da al’ummun duniya, don karfafa mu’amala tsakanin wayewar kan al’ummmin kasa da kasa, da kuma inganta zaman lafiya da ci gaban duniya.

Game da kare kayan tarihi na duniya kuwa, Lin Jian ya ce, Sin tana da abubuwan tarihi 57, wadanda aka saka a jerin kayan tarihi na duniya, kuma wannan adadi ya zama na biyu a duniya. Kaza lika Sin tana son sanya hikima, da karfinta don habaka ci gaban kayan tarihi na duniya ba tare da kasala ba.

Game da binciken gano ko motoci masu aiki da lantarki kirar kasar Sin sun samu tallafi daga gwamnatin Sin din ko a’a, wanda EU ta kuduri aniyar gudanarwa kuwa, Lin Jian ya ce, Sin na kira ga EU da ta gaggauta dakatar da binciken, don gujewa gurgunta dangantakar kasuwanci, da zaman lafiya a tsarin samar da kayayyaki, da ayyukan masana’antu tsakanin Sin da EU.

Don gane da zargin da Amurka ta yayata cewa wai “Sin na haifar da barazanar makaman nukiliya”, Lin Jian ya ce, Sin na shawartar Amurka da ta ci gaba da rage yawan makaman nukiliyarta bisa gaskiya, maimakon jefa zargin hakan ga sauran kasashe.

Sai kuma batun taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar BRICS, wanda aka gudanar kwanan nan, inda Lin Jian ya ce, ya kamata a daga matsayin kungiyar BRICS zuwa wani sabon tsarin hadin gwiwa na bangarori daban-daban, bisa sabbin kasuwanni da kasashe masu tasowa, wanda ke bude wa kowa kofa, tare da kasancewa damar cudanyar kasa da kasa.

Game da “Ra’ayoyi shida” na Sin da Brazil, don gane da warware rikicin Ukraine ta hanyar siyasa, wadanda suka samu karbuwa tsakanin kasashe da dama na duniya kuwa, Lin Jian ya ce, Sin tana maraba da karin kasashe masu goyon baya, da kuma rungumar “Ra’ayoyin shida”. (Safiyah Ma)

People are also reading