Home Back

Fada ya rincabe a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Congo

dw.com 2 days ago
Hoto: Moses Sawasawa/AP Photo/picture alliance

Fada ya rincabe a lardin Kivu na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Congo a Juma'ar nan, tsakanin dakarun sojin gwamnatin kasar da na 'yan tawayen M23, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya rawaito.

Fadan dai ya kazanta ne a yankin Kanyabayonga na lardin Kivu, mai nisan kilomita 100 da birnin Goma, wanda 'yan tawayen M23 masu samun goyon bayan Rwanda suka jima da yi wa kawanya.

Rikicin dai ya tilastawa mazauna yankin tsere wa muhallansu don kare rayukansu.

Wani rahoto da ofishin kare hakkin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniyar ya fitar a Juma'ar nan, ya nuna cewa 'yan tawayen M23 na ci gaba da nausawa cikin arewacin Kivu don mamaye shi, musamman ma yankin Lubero.

People are also reading