Home Back

Duk Da Farfadowar Darajar Naira, Tsadar Kaya Na Ci Gaba Da Lulawa Sama

leadership.ng 2024/5/14
Duk Da Farfadowar Darajar Naira, Tsadar Kaya Na Ci Gaba Da Lulawa Sama

Duk da karuwar darajar naira, tsadar farashin kayayyaki ta ci gaba da lulawa sama a Nijeriya. A yanzu dai ana sayar da kowacce dalar Amurka guda daya kan naira 1 a kasuwannin bayan fage.

A cewar hukumomi, wannan matakin ci gaba ne kuma tagomashi ne da naira ke samu a kan dala, sai dai duk da wannan matakin, tsadar kayan masarufi bai ragu ba, illa ma karuwa da ya yi.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar kiddiga ta kasa (NBS) ta ce farashin kayan masarufi ya sake yin tashin gwauron zabi da kaso 33.20 a cikin 100 a watan Maris din 2024, idan aka kwatanta da kaso 31.70 cikin 100 a watan Fabrairu.

Ci gaban tagomashin da aka samu a kan darajar naira kan dalar Amurka ya samu ne tun a ranar 26 ga watan Satumban 2023.

A cikin shekara guda an samu karuwar hauhawar farashi da kaso 11.16, idan aka kwatanta da kaso 22.04 cikin dari a watan Maris din 2023.

A cewar rahoton, tashin farashin kayan abinci ya haura da kaso 40.01 a cikin shekara guda a watan Maris, sama da kaso 15.56 cikin dari da aka samu kari domin a watan Maris na 2023 farashin na kaso 24.45.

Kayan da suka tashin sun hada da na farashin makamashi zuwa kaso 25.90 cikin dari a watan Maris, inda ya karu da kaso 6.26 sabanin kaso 19.63 da aka samu a watan Maris na 2023.

Hukumar NBS ta ce tashin farashin kayan abinci ya samu asali ne sakamakon karuwar farashin gari, gero buredi da nau’ikan hatsi, doya, dawa, da kuma busasshen kifi.

Sauran abubuwan da suka janyo tashin farashin kayan abincin sun kuma kunshi mangyade, nama, hanta, madara, bombita, ruwan lelon da dai sauransu.

Bugu da kari, tsadar kudin sufuri da zirga-zirga su ma sun kara ba da gudunmawa wajen tashin farashin kayan masarufi a Nijeriya, kamar yadda rahoton hukumar NBS ta tabbatar.

Tambayen da Nijeriya suke ci gaba da yi shi ne, me ya sa farashin kayayyaki ba su sauko kasa ba? Domin a baya ana cewa tashin farashin dala ne ya haifar da tsadar kayayyaki.

Wasu daga cikin ‘yan kasuwa sun bayyana cewa saukar farashin dal aba zai iya sauko da farashin kayayyaki nan take ba, domin mafi yawancinsu suna tare da tsofaffin kayayyaki ne wanda suka siyo a lokacin tsadar farashin dala, sai sun iya sayar da wadannan kayayyaki ne kafin za su sayo sabbin kaya a farashi mai rahusa.

People are also reading