Home Back

Amurka ta ƙara yawan lada don kwarmata wurin da 'Sarauniyar Kirifto' take

bbc.com 5 days ago
..

Asalin hoton, Facebook/Dr.RujaIgnatova

Hukumomin Amurka sun ƙara yawan tukwici zuwa dala miliyan biyar ga duk wanda ya kwarmata bayanan da za su kai ga kama matar da ake yi wa laƙabi da Sarauniyar Kirifto wato Ruja Ignatova wadda ta yi ɓatan dabo, bayan damfarar da ta yi ta dala biliyan 4.5.

Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, FBI, na neman Ruja Ignatova, mai shekaru 44 wadda ƴar asalin ƙasar Bulgeria ce haihuwar Jamus, bisa tuhumar kitsa badaƙalar kuɗaɗen kirifto da ake kira OneCoin masu yawan dala biliyan 4.5

Tun dai shekarar 2017 ne Sarauniyar ta yi ɓatan dabo lokacin da jami'an Amurka suka sanya hannu kan sammacin neman ta kuma masu bincike suka fara bincike a kanta.

Makonni uku da suka gabata, wasu shirye-shiryen BBC suka bayyana alaƙarta da masu aikata laifi a ƙasar Bulgeria da kuma shugaban ƴan ƙungiyar mafiya da ke cikin ɓatan nata dumu-dumu da muka zargin kisanta da aka yi.

To sai dai hukumomi sun ci gaba da yin bibikon neman misis Ignatova.

A 2022, hukumar FBI ta ƙara sunan Ignatova a jerin mutum 10 da take nema ruwa a jallo, inda hukumar ta yi tayin ladan dala 100,000 kafin daga bisani ta ƙara tukwicin zuwa dala 250,000 ga duk wanda ya kwarmata inda take.

A ramar Larabar da ta gabata ne kuma aka sake ruɓanya ladan sau 22, a ƙarƙashin ofishin da ke bayar da lada domin kama masu laifukan ƙasa da ƙasa.

"Za mu bayar da ladan har dala miliyan biyar ga kwarmata bayanan da za su kai ga kama ko kuma gurfananr da Ruja Ignatova ƴar ƙasar Jamus wadda aka fi sani da "Sarauniyar Kirifto' bisa rawar da ta taka dangane da wata badaƙalar da ta kasance ɗaya daga cikin mafi girma a tarihi," in ji mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Mathew Miller.

Yanzu haka dai Ignatova ce mace ɗaya tilo da shirin bayar da lada domin neman masu aikata laifukan ƙasa da ƙasa ke nema ruwa a jallo.

Akwai irin wannan tukwici na dala miliyan biyar ga duk wanda ya kwarmata bayanan da za su kai ga kama Daniel Kinahan wanda shugaba ne na wani gungun masu safarar ƙwaya a Turai.

Harwayau irin wannan kuɗin ne aka sa kan Semion Mogilevich da ake zargin madugun masu aikata laifi ne da ke zaune a ƙasar Rasha da kuma Yulan Adonay Archaga Carias wanda aka fi sani da Porky, wanda shi ne mutumin da ya fi kowa girma a ƙungiyar ɓatagari ta MS-13 a ƙasar Honduras.

Hukumomi a Jamus dai tuni sun tuhumi Ruja Ignatova.

A ƙasar Bulgaria kuwa inda daga babban birninta, Sofia ne aka gudanar da tsarin kirifton na OnceCoin, wani jami'a a ranar Laraba ya ce za su tuhume Ignatova duk da ta yi ɓatan dabo.

Jamie Barlett, wanda shirinsa na BBC ya ja hankalin duniya ga labarin Ruja Ignatova, ya yi imanin cewa an yi ƙarin ladan da aka sanya ne saboda mutanen da ke ɓoye ta.

"Hukumar FBI ta sauya tunaninta zuwa kan waɗanda suke ɓoye da Dr Ruja domin jan hankalinsu su tona asirinta.

"Dala 100,000 da aka sanya da farko ba za su sa masu laifi su kira layin wayar FBI domin tsegunta bayanai ba. To amma yanzu dala miliyan biyar ka iya sanya su yin hakan.

"Za mu fahimci ko tukwicin ya yi aiki ko kuma bai yi ba a nan da wasu ƴan makonni."

Ita dai Ruja Ignatova wadda ita ce shugabar kamfanin kudin kirifto na OnCoin wanda na jabu ne, ita ce mace da hukumar binciken laifuka ta Amurka, FBI ta fi nema ruwa a jallo. Ta damfari jama'a biliyoyin kuɗaɗe sannan ta yi ɓatan dabo. Sabbin shaidu sun bayyana abubuwan da ka iya faruwa. Amma abin tambaya a nan shi ne ko ta ɓata ne ko kuma an kashe ta?

To sai dai neman da ake yi mata ruwa a jallo ya ɗauki wani sabon salo lokacin da labarin da ke zargin an kashe ta ya bayyana.

People are also reading