Home Back

Yadda Koriya ta Arewa ke tura bola zuwa Koriya ta Kudu ta balan-balan

bbc.com 2024/7/5

Asalin hoton, Reuters

Hukumomi a Koriya ta Kudu sun shawarci mutane su zauna cikin gidajensu
Bayanan hoto, Hukumomi a Koriya ta Kudu sun shawarci mutane su zauna cikin gidajensu
  • Marubuci, Kelly Ng
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

Koriya ta Arewa ta tura manyan balan-balan aƙalla guda 260 ɗauke da shara zuwa maƙwafciyarta Koriya ta Kudu, wani lamari da ya kai ga cewa hukumomin Koriya ta Kudu sun gargaɗi al'ummarsu su zauna cikin gida.

Haka nan Koriya ta Kudun ta gargaɗi al'ummar tata da su kauce wa taɓa bala-balan ɗin da sharan da yake ɗauke da ita kasancewar suna ɗauke da 'ƙazanta da kuma bola".

Yanzu haka an nazari kan balan-balan ɗin waɗanda suka faɗa a yankuna takwas daga cikin yankuna tara na ƙasar.

Dukkanin ƙasashen biyu sun riƙa amfani da irin waɗannan balan-balan wajen tura saƙonnin fargafaganda zuwa cikin juna tun bayan yaƙin ƙasashen biyu a cikin shekarun 1950.

Rundunar sojin Koriya ta Arewa ta kuma ce tana bincike domin gano ko akwai wasu takardun yaɗa farfaganda da aka ƙunso a cikin balan-balan ɗin da maƙwafciyar tata ta turo.

Wannan lamari na zuwa ne bayan Koriya ta Arewa ta yi barazanar cewa za ta rama abin da masu fafutika na Koriya ta Kudu ke yi na tura takardun farfaganda zuwa cikin ƙasarta.

A ranar Lahadi, ƙaramin ministan tsaron Koriya ta Arewa, Kim Kang Il ya bayyana a cikin wata takarda cewa: "Kwanan nan tarin bola da shara za su cika a kusa da bakin iyuaka, daga nan mutanen Koriya za su gane wahalar da ake sha wajen kwashe su".

A ranar Talata, mazaunan arewacin babban birnin Koriya ta Kudu da kuma na kusa da kan iyaka suka samu saƙonni daga gwamnatin kan cewa su "guje wa yin hidimominsu a waje".

Kuma an buƙace su su kai rahoto ga sojoji ko hukumar ƴansanda idan suka ci karo da "wani abu da ba su gane ba".

Asalin hoton, South Korean military

Hukumomi na nazari kan shara da bolar da balan-balan ɗin ya zubar
Bayanan hoto, Hukumomi na nazari kan shara da bolar da balan-balan ɗin ya zubar

Hotuna da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna wasu ledoji da aka ƙulla a jikin bala-balan na sauka ɗauke da takardar goge bahaya da ƙasa mai launin baƙi da tsofaffin batura da wasu abubuwan da dama.

Za a iya ganin jami'an tsaron soji da ƴansanda wasu daga cikin hotunan.

Kamfanin dillancin labarun Koriya ta Kudu, Yonhap ya ruwaito cewa da alama wasu daga cikin ledojin na ɗauke da bahaya saboda ƙasar baƙin ƙirin ce.

Rundunar sojin Koriya ta Kudu ta yi tir da lamarin inda suka bayyana shi a matasin "karya dokar ƙasa da ƙasa ƙarara".

"Wannan abu mummunar barazana ce ga lafiyar al'ummarmu. Koriya ta Arewa ce za a kama da laifi a kan duk wani abu da ya faru, kuma muna gargaɗin Koriya ta Arewa ta dakatar da wannan mummunan al'amari nan take," in ji rundunar sojin.

Baya ga saƙonnin farfaganda da ƴan hanƙoro na Koriya ta Kudu ke turawa zuwa Koriya ta Arewa ta hanyar balan-balan, sun kuma riƙa tura abubuwa kamar kuɗi da fina-finan da aka haramta kallo a ƙasar da kuma fanken 'Choko Pies', wani abincin Koriya ta Kudu wanda aka haramta ci a Koriya ta Arewa.

A farkon wannan mako, wani ɗan hanƙoro na ƙasar Koriya ta Kudu ya ce ya tura manyan balan-balan ɗauke da takardu masu saƙonnin adawa da gwamnatin Koriya ta Arewa da kuma bidiyon waƙoƙin Koriya ta Kudu - zuwa cikin Koriya ta Arewa.

A watan Disamban 2020 majalisar dokokin Koriya ta Kudu ta amince da wata doka wadda ta haramta tura takardu masu ɗauke da saƙon farfaganda zuwa cikin Koriya ta Arewa, sai dai wasu sun soki hakan, suna cewa ya yi karan-tsaye ga ƴancin faɗin albarkacin baki.

Ita ma Koriya ta Arewa ta tura wasu balan-balan ɗin zuwa Koriya ta Kudu ɗauke da saƙonnin sukar gwamnatin. A shekara ta 2016 Koriya ta Arewar ta tura irin waɗannan balan-balan zuwa cikin Koriya ta Kudu, wadanda aka ce suna ɗauke da takardun da aka goge bahaya, da kwanson sigari da bola.

Ƴansandan Koriya ta Arewa sun bayyana sharan a matsayin 'masu guba ga halitta.'

People are also reading