Home Back

MASIFAR TSADAR RAYUWA DA RASHIN CINIKI: An rufe katafaren kantin Shoprite a Abuja

premiumtimesng.com 2024/7/2
MASIFAR TSADAR RAYUWA DA RASHIN CINIKI: An rufe katafaren kantin Shoprite a Abuja

Watanni shida bayan rufe katafaren kantin Shoprite a Kano, yanzu kuma an sanar da kulle wani tangamemen kantin Shoprite da ke Zone 5, a Abuja, daga ranar 30 ga Yuni.

Sanarwar dai na ɗauke da sa hannun Babban Shugaban Hada-hada na Shoprite, Folakemi Fadahunsi, wadda aka fitar a ranar Litinin.

Wani ma’aikacin kantin ya tabbatar da cewa lamarin kulle kantin kwata-kwata gaskiya ne.

An dai danganta daina hada-hadar kasuwanci a Shoprite bayan an yi lissafin saye da sayarwa, faɗuwa da riba ko maida uwar kuɗi, wadda aka gano cewa a kullum ana kwana a ciki, ko kuma ciko na biyo gyartai.

Sanarwar ta ƙara da cewa daga yanzu kada wani mai kaya ya ƙara kai masu tallar kaya, saboda sun daina kwata-kwata.

Kantin dai ya na kan titin Novare, Wuse Central Mall, Abuja.

Sanarwar ta ce kantin wanda ke kusa da Hedikwatar PDP a Wadata Plaza, zai yi lissafin waɗanda ke bin sa bashi, domin ya biya su nan da kwanaki 60 daidai.

Idan ba a manta ba, a Jihar Enugu an taɓa kulle Shoprite saboda kasa biyan haraji, da kauce wa biyan haraji.

A Kano ma tun cikin watan Janairu aka kwashe komai a kantin Shoprite da ke Ado Bayero Mall, kan titin Zoo Road.

A Jihar Delta kuwa, ma’aikatan Shoprite sun taɓa yin zanga-zanga saboda rashin biyan su kuɗaɗen alawus-alawus ɗin su na ƙarshen shekara.

Tun bayan cire tallafin fetur dai matsalar tsadar rayuwa da tulin haraji da matsalar tsaro na tilasta wa manyan kamfanoni da masana’antun ƙasashen waje ficewa daga Najeriya. Lamarin da ke ƙara haifar da sallamar ɗimbin ma’aikata daga aiki a kamfanonin da masana’antun ko cibiyoyin hada-hadar.

Wani masanin tattalin arziki kuma tsohon Daraktan Bincike a Cibiyar Cinikayya da Kasuwanci ta Jihar Legas, Dakta Vincent Nwani, ya ce Najeriya ta yi asarar ciniki zai kai na Naira tirliyan 94, sakamakon ficewar manyan kamfanoni da masana’antu, irin su Standard Biscuits Nigeria Limited, NASCO Fiber Product Ltd, Union Trading Company, Nigeria Ltd, Deli Foods Nigeria Ltd, Tower Aluminum Nigeria PLC, Framan Industries Ltd da sauran manyan kamfanonin da suka fice a cikin 2022, 2023, da 2024.

Akwai dai Shoprite a Abuja da suka haɗa da na Jabi Lake, Aleta Bridge kusa da Lugbe.

People are also reading