Home Back

Ederson zai bar City, Barca na son Cancelo, Man United na daf da daukar Lusale

bbc.com 2024/10/6
.

Asalin hoton, Manchester City

Manchester City na sa ran Saudiyya ta kai tayin mai tsaron gidanta Ederson, yayin da Flamengo ke tattaunawa da West Ham kan neman Lucas Paqueta, Marc Cucurella ya yi kokarin shawo kan Nico Williams ya koma Chelsea.

Manchester City na jiran Saudiyya, ta mika tayin mai tsaron gidanta Ederson, inda take sa ran samun fam miliyan 30 kan dan wasan na Brazil, wanda ake alakanta shi da Al-Nassr. (Talksport)

Marseille na da kwarin gwiwar shiga gaban zawarcin Lazio wajen siyan dan wasan gaban Manchester United Mason Greenwood bayan kungiyar ta Seria A tayi tayin £17m kan dan wasan mai shekaru 22 (Mail)

Flamengo ta fara tuntubar West Ham game da sayen dan wasan Brazil Lucas Paqueta, mai shekara 26, kuma kungiyoyin biyu sun fara tattaunawa. (Globo)

Barcelona ce kan gaba wajen sayen dan wasan gaba na Athletic Bilbao da Spaniya Nico Williams, inda Arsenal da Chelsea ke fuskantar hadarin rasa dan wasan mai shekaru 21. (Football Insider)

Dan wasan baya na Chelsea Marc Cucurella, mai shekara 25, ya ce yana kokarin shawo kan abokin wasansa na Spain Williams ya koma kungiyar (Sport Spanish)

Dan wasan baya na Lille Leny Yoro yana son komawa Real Madrid kuma dan kasar Faransan mai shekaru 18 yayin da Liverpool da Paris St-Germain ke sa ran cimma matsaya idan yarjejeniyar ta ruguje. (Fabrizio Romano)

Dan wasan bayan Aston Villa Matty Cash da alama zai yi wuya ya koma AC Milan duk da rahotannin da ke alakanta dan wasan na Poland mai shekaru 26 da komawa kungiyar ta Seria A. (Birmingham Live)

Barcelona na zawarcin dan wasan Manchester City Joao Cancelo bayan dan wasan bayan na Portugal mai shekara 30 ya shafe kakar wasan da ta wuce a matsayin aro a kungiyar ta Spaniya. (SportsMole)

Juventus na son karfafa tsakiyarta, wajen daukar dan wasan Atalanta mai shekaru 26 dan kasar Holland Teun Koopmeiners. (La Gazzetta dello Sport)

Manchester United na dab da sayen Samuel Lusale dan kasar Slovakia mai shekaru 16 daga Crystal Palace. (Mirror)

Yunkurin Newcastle United na neman dan wasan Everton Dominic Calvert Lewin, mai shekara 27, ya ruguje bayan da Magpies ta kasa siyar da dan wasanta na Ingila Callum Wilson. (Telegraph)

Ajax, Nice, Rennes da Olympiakos na daga cikin kungiyoyi da dama da ke son dauko dan wasan bayan Portugal Cedric Soares mai shekaru 32, wanda ke zaman kansa, bayan karewar kwantiraginsa da Arsenal. (Standard)

Manchester United na son siyar da dan wasan tsakiya dan kasar Holland Donny van de Beek na dindindin a wannan bazara maimakon ta rasa shi a kyauta lokacin da kwantiragin dan wasan mai shekaru 27 zai kare a bazara mai zuwa. (Manchester Evening News)

Dan wasan gaban Chelsea Romelu Lukaku, mai shekara 31, yana son haduwa da kocin Napoli Antonio Conte, wanda ya horar da dan wasan gaban na Belgium a Inter Milan. (Corriere dello Sport)

Napoli ta shaida wa Chelsea cewa a shirye ta ke ta rage farashin dan wasan Najeriya Victor Osimhen mai shekaru 25 kan fam miliyan 110.8. (Metro)

Dan wasan baya na Jamus Waldemar Anton, mai shekara 27, ya tsallake rijiya da baya a Borussia Dortmund kuma zai koma kungiyar daga Stuttgart ta Jamus bayan gasar Euro 2024. (Sky Sports Germany)

People are also reading