Home Back

An soke liyafar cin abinci tsakanin Justin Trudeau da Giorgia Meloni

rfi.fr 2024/4/29

An soke liyafar cin abinci tsakanin firaministan Canada Justin Trudeau da takwararsa ta Italiya Giorgia Meloni a birnin Toronto a jiya Asabar saboda "dalilai na tsaro", in ji ofishin Firaministan Canada, yayin da aka gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu a kusa da wurin da za su hadauwa.

Wallafawa ranar: 03/03/2024 - 09:40

Minti 1

Yan Sanda a harabar dakin shirya liyafar cin abinci  a Ontario na kasar Canada
Yan Sanda a harabar dakin shirya liyafar cin abinci a Ontario na kasar Canada © AFP

A cewar kafofin yada labaran Canada, daruruwan masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu ne suka taru a gaban dakin wasan kwaikwayo na Art Gallery na Ontario, a tsakiyar babban birnin kasar Canada, inda aka shirya liyafar.

"An soke taron ne saboda dalilai na tsaro," Jenna Ghassabeh, sakatariyar yada labarai na ofishin Firaministan Canada, ta tabbatar da haka ba tare da bayar da karin haske ba.

Firaministar Italia, Giorgia Meloni, da Firaministan Canada Justin Trudeau,
Firaministar Italia, Giorgia Meloni, da Firaministan Canada Justin Trudeau, © Carlos Osorio / Reuters

Firaministar Italia ta bayyana cewa sun damu matuka da halin da Falasdinwa ke ciki yanzu haka,sai dai a   cewar gidan talabijin na CBC Canada, masu zanga-zangar adawa da yadda Canada ke mayar da martani a rikicin da ya barke tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas ta Falasdinu , ya sa wasu daga cikin masu halartar wannan liyafar kauracewa shiga dakin  taro.

Firaministan Canada Justin Trudeau,
Firaministan Canada Justin Trudeau, © Sean Kilpatrick / AP

An bayyana mutane kusan 200 zuwa 300 masu zanga-zangar da suka kasance a wurin lokacin guda.

 
People are also reading