Home Back

Abubuwa biyar game da rayuwar Sheikh Dahiru Bauchi wanda ya shekara 100

bbc.com 2024/8/21
Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Babban malamin addinin Musulunci kuma jagoraran ɗariƙar Tijjaniyya a Najeriya Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya cika shekara 100 da haihuwa a ranar Litinin, 2 ga watan Muharram 1446.

Manyan mutane ciki har da shugaban Najeriya, Bola Tinubu ne suka taya babban malamin murna.

Sheikh Ɗahiru Bauchi ya shahara a matsayin malamin addinin Musulunci a Najeriya da ƙasashe daban-daban na duniya.

Ga wasu muhimman bayanai game da malamin:

Haihuwa

An haifi Sheikh Dahiru Usman Bauchi a ranar Laraba 28 ga watan Yunin shekarar 1927 wanda ya yi daidai da 2 ga watan Al Muharram shekarar 1346 a garin Nafada jihar Gombe, arewa maso gabashin Najeriya.

Mahifinsa mutumin jihar Bauchi ne, mai suna Alhaji Usman Adam, wanda shi ma "babban malami ne kuma gwanin karatun Ƙur'ani".

Mahaifiyarsa kuma sunanta Hajiya Maryam, 'yar jihar Gombe ce, kuma dukkannin su Fulani ne.

Malamin ya rayu a gaban mahaifinsa kuma ya haddace Alkur'ani a wurin mahaifinsa, kana ya tura shi ya shiga duniya don ya gyara tare da karo karatunsa.

A hirarsa da BBC a shirin Ku San Malamanku, malamin ya ce ya kuma samu nasarar kara fahimtar haddar Alkura'ani mai girma a wuraren da ya tafi neman karatun.

Iyali

A tattaunawarsa da BBC, ɗaya daga cikin ƴaƴan Shehin malamin, Sheikh Bashir Dahiru Usman Bauchi ya ce a yanzu yawan ƴaƴan da malamin ya haifa sun kai kimanin 90, sannan yana da jikoki da suka zarce 100.

Babban ɗa namiji na malamin shi ne Muhammad Bello, wanda ya rasu tun yana ƙarami, sai kuma mai bi masa, Dakta Hadi Dahiru Bauchi.

Ya bayyana cewa akwai ƴaƴan malamin sama da 70 waɗanda suka haddace Alƙur'ani, kuma jikokinsa sama da 100 ne suka haddace Ƙur'anin.

Matan Sheikh Dahiru Bauchi

Sheikh Bashir ya ce a yanzu haka Dahiru Bauchi na da mata huɗu. Su ne:

Hajiya Fatima (Nana)

Hajiya Khadija (Inna)

Hajiya A'isha

Hajiya Maman Hamrat

Malaman Sheikh Dahiru Bauchi

Sheikh Dahiru Bauchi ya shaida wa BBC cewa babban malaminsa shi ne mahaifinsa, amma kuma ya ce ya fara karatu a hannun Malam Baba Sidi, da Malam Saleh, da Malam Baba Dan Inna.

Kana ya ce ya kuma je garin Zaria wajen su malam Abdulkadir nan ma ya taɓa karatu, kana ya je garin Kano inda ya sadu da manyan malaman Kano ya kuma yi karatu a wajen Malam Shehu Mai Hula da Shehu Malam Tijjani da kuma Shehu Atiku.

Play video, "Ku San Malamanku tare da Sheikh Dahiru Usaman Bauchi", Tsawon lokaci 10,38
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon shirin Ku San Malamanku tare da Sheikh Dahiru Bauchi

Dangantakarsa da Sheikh Ibrahim Inyass

Sheik Dahiru Usman Bauchi ya kuma shaida wa BBC cewa, baya ga kasancewa almajirin Sheikh Ibrahim Inyass, akwai ƙarin dangantaka mai ƙarfi a tsakaninsu.

Ya ce: ''Alhamdulillah baya ga zama almajirin Sheikh Ibrahim na kuma zama khadiminsa, kana na zama surukinsa, don na auri ƴaƴansa har sau biyu, na auri ɗaya bayan ta rasu ya sake ba ni auren ɗaya.''

Kana malamin ya ce baya ga haka, yana ƙauna tare da mutunta malamai a ko'ina suke, musamman malaman Tijjaniyya.

''Babu abin da ke faranta min rai irin na ga Musulunci ya bunƙasa, in ga ɗarikar Tijjaniyya ta bunƙasa,'' in ji malamin.

Abubuwan da Sheikh Dahiru Bauchi ya fi so

Karatun Alƙur'ani

Sanya fararen kaya

People are also reading