Home Back

Sojoji Sun Lalata Masana’antar Sarrafa Burodin ‘Yan Ta’adda A Borno

leadership.ng 2024/5/19
Sojoji Sun Lalata Masana’antar Sarrafa Burodin ‘Yan Ta’adda A Borno

Dakarun sojin Nijeriya sun lalata wata masana’antar sarrafa burodi ta ‘yan ta’addan ISWAP a yankin Maisani na Timbuktu a karamar hukumar Damboa ta j6ihar Borno. 

Hadin gwiwar rundunar ta musamman ta CJTF ne, suka gano masana’antar, yayin wani wani samame da suka kai a jiya Lahadi.

Wannan dai na cikin wata sanarwa da mai nazari kan harkokin tsaro, Zagazola Makama ya fitar.

A cewar Makama, “Majiyoyi sun bayyana cewa dakarun sun lalata masana’antar, kuma kayayyakin da aka kwato a yayin samamen sun hada da kayan abinci, injin sarrafa burodi daya, da kuma kayan hadin burodi masu tarin yawa.”

Wannan nasarar na zuwa ne bayan da dakarun sojin Nijeriya suka ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan ta’adda a yankin.

“Wadannan ‘yan ta’addan na da alhakin kai hare-hare, farmaki da birne bama-bamai musamman a titunan Damboa, babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri da sauran hanyoyi irin su Askira, Buratai, Buni Yadi tare da lalata hanyar samar da wutar lantarki a Borno da Jihar Yobe.”

People are also reading