Home Back

Wani na son tayar da abin fashewa a ofishin jakadancin Iran

dw.com 2024/5/2
Hoto: Benoit Tessier/REUTERS

'Yan sandan Faransa sun killace ofishin jakadancin Iran da ke birnin Paris, bayan da wani mutum ya yi ikirarin tayar da wani abin fashewa da ke jikinsa a ciki.

Gidan Rediyon Faransa Europe 1, ya wallafa a shafinsa na X cewa jami'an tsaron sun yi wa harabar ofishin jakadancin kawanya yanzu haka, sannan sun umarci jama'a su kaucewa wurin baki-daya.

People are also reading