Home Back

Dalilin 'Yan Sanda Na Tura Karin Jami'an Tsaro a Fadar Sanusi II da Aminu Ado

legit.ng 2024/7/7
  • Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta fito ta yi magana kan dalilin da ya sanya aka ga ƙarin jami'an tsaro a fadar Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero
  • Kwamishinan ƴan sandan jihar mai barin gado, AIG Usaini Gumel, ya bayyana cewa an tura ƙarin jami'an tsaron ne domin samar da tsaro a wuraren guda biyu
  • Ya bayyana cewa jami'an tsaron an tura su ne domin tabbatar da zaman lafiya har zuwa lokacin da za a kawo ƙarshen rikicin na masarautar Kano

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Rundunar ƴan sanda ta bayyana dalilin da ya sa ta tura ƙarin jami’anta zuwa fadar da Muhammmadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero da suke a Kano.

Rundunar ƴan sandan ta tura ƙarin jami'ai zuwa fadar Ƙofar Kudu da fadar Nasarawa waɗanda ke a cikin birnin Kano.

'Yan sanda sun tura karin jami'an tsaro fadar Sarkin Kano
'Yan sanda sun tura karin jami'an tsaro zuwa fadar Sarkin Kano Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Aminu Ado Bayero, Kano State Police Command Asali: Facebook

AIG Usaini Gumel, kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, ya tabbatar da tura ƙarin jami’an tsaron zuwa fadar sarakunan guda biyu a wata hira da aka yi da shi ranar Litinin, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa aka tura jami'ar fadar Sarkin Kano?

Usaini Gumel, wanda shi ne kwamishinan ƴan sandan Kano mai barin gado ya bayyana cewa, tura jami'an tsaron na da nufin tabbatar da zaman lafiya har zuwa lokacin da za a warware rikicin masarautar.

Ya ƙara da cewa an baza jami'ai masu ɗauke da kayan aiki domin tunkarar duk wata barazana a wuraren, rahoton PM News ya tabbatar.

"An baza jami’an tsaro domin tabbatar da tsaro a fadar Kofar Kudu, gidan sarki Muhammadu Sanusi II, da kuma fadar Nasarawa gidan sarki Aminu Ado Bayero.

- AIG Usaini Gumel

Kwamishinan ƴan sandan ya nemi goyon bayan al'ummar birnin tare da roƙonsu su bayar da bayanan da za su taimaka wajen samar da zaman lafiya da ci gaba a jihar.

Lauya ya ba Gwamna Abba shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani fitaccen mai sharhi kan al'amuran yau da kullum, Law Mefor, ya ce gwamnatin jihar Kano ba ta ikon sauya hukuncin da kotu ta yanke.

Mefor ya bayyana cewa idan gwamnatin Abba Kabir tana da ja da hukuncin babbar kotun tarayya, kamata ya yi ta ɗaukaka ƙara ba wai ta take umarnin doka ba.

Asali: Legit.ng

People are also reading