Home Back

Yajin Aiki: NAHCON Ta Gargadi NLC Kan Janyo Cikas Ga Jigilar Maniyyata

leadership.ng 2024/7/3
NAHCON

Hukumar kula da jin dadin alhazai ta kasa (NAHCON), ta gargadi kungiyar kwadago (NLC) dangane janyo cikas ga ci gaba da aiki jigilar maniyyata daga nan gida Nijeriya zuwa kasar Saudiyya Arabiyya sakamakon yajin aiki. Mataimakiyar daraktan sashin yada labarai na NAHCON, Misis Fatima Usara, ita ce ta yi gargadin a wata sanarwar da ta fitar a Abuja.

Usara ta nemi NLC da ta gane hatsarin da ke cikin janyo cikas da tarnaki ga jigilar maniyyatan aikin hajjin bana. Ta nuna cewa kamata ya yi NLC ta taimaki duk wani motsi na samun nasarar kwasan maniyyata ba wai janyo cikas ba.

“Bayanai sun riski NAHCON da ke nuni da cewa akwai shirye-shiryen da wasu bangaren NLC ke yi na kokarin kawo cikas na jigilar maniyyata aikin hajji da ake kan gudanarwa.
“Wannan na zuwa ne duk da kyakkyawar fahimtar juna da aka cimma na cewa babu abun da zai shafi jiragen da ke jigilar maniyyata sakamakon shiga yajin aiki.

“Hukamarmu ta jinjina wa damuwar da NLC ta nuna kan tabbatar da walwala da jin dadin mambobinta, amma NAHCON na son a mutunta damar zuwa aikin hajji ga Musulman da suka samu dama.
“Hukumar ta shawarci NLC da ta yi taka-tsan-tsan ka da ta yi katsalandan wajen janyo cikas domin mutunta addinin Musulunci.

“Janyo duk wata cikas ko jinkiri ga aikin jigilar alhazai ka iya janyo a tauye wa Musulmai masu niyyar zuwa aikin hajji hakkinsu da ‘yancinsu na yin ibada lura da dan kankanin lokacin da aka ware domin rufe filayen jiragen Jeddah da Madinah ga maniyyata,” sanarwar ta shaida.

A kalla maniyyata dubu 65,500 daga Nijeriya ne ake sa ran za su gudanar da aikin hajji a can kasa mai tsarki a shekarar 2024.

NAHCON ta yi jigilar maniyyata sama da 38,805 zuwa Saudiyya a jirage 92 daban-daban.

People are also reading