Home Back

Alhazan Yobe 1,332 Sun Karbi N179.8m Daga Gwamnatin Jihar

legit.ng 2024/7/1
  • Gwamnatin jihar Yobe karƙashin Gwamna Mai Mala Buni ta cika alƙawarin da ta ɗauka na tallafawa alhazan jihar 1,332
  • Shugaban hukumar jin daɗin alhazai na jihar, Alhaji Mai Aliyu ya ce kowane mutum ɗaya daga cikin mahajjatan ya samu alawus na N135,000
  • Ya ce a halin yanzun an kammala kwashe alhazan jihar zuw Madinah kuma galibi sun kama hanya zuwa Makkah sauran kaɗan ya rage

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Yobe - Hukumar Alhazai ta jihar Yobe ta ce ta biya tallafin Naira miliyan 179.8 da gwamna Mai Mala Buni ya amince a rabawa maniyyata 1,332 na jihar.

Gwamma Mai Mala Buni ya bai wa maniyyatan wannan tallafi ne domin taimaka masu su gudanar da aikin hajjin bana 2024 cikin farin ciki da walwala.

Gwamna Mai Mala Buni.
Gwamnatin Yobe ta cika alƙawari, ta bai wa alhazan jihar tallafi Hoto: Mai Mala Buni Asali: Twitter

Shugaban hukumar alhazan Yobe, Alhaji Mai Aliyu ne ya bayyana haka a lokacin da yake yiwa gwamnan karin bayani kan jigilar maniyyatan zuwa ƙasa mai tsarki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce kowane mahajjaci ya samu N135,000 na alawus alawus na tafiya kamar yadda gwamna ya bayar da umarni, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

A cewarsa, dukkan maniyyatan da jami’an hukumar jin daɗin alhazai ta jihar, an kammala jigilarsu zuwa kasar Saudiyya.

"Sun sauka lafiya a Madina, birni na biyu mai tsarki don gudanar da ayyukan ibada da ziyarce-ziyarce, kuma a yanzu sun wuce Makka, in ban da ‘yan kadan da ke Madina har yanzu,” Inji Aliyu.

Shugaban ya bayyana cewa hukumar ta samu damar kama otal-otal na kusa, waɗanda ƴar tafiya ce kaɗai zata kai ka masallatai masu tsarki a Madina da Makkah. 

Ya ce dukkan maniyyatan suna cikin koshin lafiya kuma suna yiwa gwamna da gwamnatin jihar Yobe addu'ar fatan alheri, Allah ya karawa jihar Yobe da Nijeriya zaman lafiya.

Gwamna Buni ya yabawa hukumar da kamfanonin jiragen sama bisa yadda suka tabbatar da ankammala jigilar alhazai a kan lokaci.

Ya kuma bukaci hukumar ta kula da alhazan jihar Yobe yadda ya kamata kuma ta bai wa walwala da jin daɗinsu fifiko.

Gwamna Buni ya yi addu’ar Allah ya karbi wannan ibada ta alhazan mu da kuma addu’o’in da suke yi kuma ya dawo da su gida lafiya.

Da gaske EFCC ta fara binciken Kwankwaso?

A wani rahoton kuma shugaban NNPP na jihar Kano ya musanta rahoton cewa hukumar EFCC ta taso Kwankwaso kan wasu kuɗaɗen kamfe.

Hashimu Dangurawa ya ce rahoton ƙarya ne kuma wasu maƙiyan Kwankwaso suka kirkiro shi domin ɓata masa suna.

Asali: Legit.ng

People are also reading