Home Back

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 7 A Wani Sabon Hari A Jihar Neja

leadership.ng 2024/6/29
‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 7 A Wani Sabon Hari A Jihar Neja

Akalla mutum 7 ne suka mutu a wani sabon hari da wasu ‘yan bindiga suka wani yanki a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Daily Trust ta rawaito cewa maharan sun fille kawunan mutane biyu, Kabiru Salihu da Abubakar Karaga.

Daga cikin kauyukan da aka kai wa harin a tsakanin ranar Alhamis zuwa Juma’a, akwai Lanta da Bassa da Kasimani da Unguwan-Madi da Makuda da dai sauransu, inda aka ce an kona gidaje da dabbobi da dama.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta saboda barazanar tsaro ta ce, “Baki daya mutane bakwai ‘yan ta’addar suka kashe a Bassa.”

An tuntubi Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, amma bai samu ba har ya zuwa lokacin hada wannan labarin.

People are also reading