Home Back

An kaddamar da gwamnatin hadaka a Afirka ta Kudu

dw.com 2024/10/6
Südafrika Kapstadt | Cyril Ramaphosa und John Steenhuisen
Hoto: South African GCIS/AP/picture alliance

Jam'iyyar African National Congress wacce ke mulkin kasar tun shekarar 1994 ta sami ministoci 20 da suka hada da ministan kudi da na tsaro da na harkokin waje da na 'yan sanda gami da na ma'aikatar shari'a.

Jam'iyyar Demokratic Alliance wato DA ta sami ministoci shidda da suka hada da ministan harkokin cikin gida da muhalli da na ayyuka, ita kuma jam'iyyar IFP da sauran kananan jam'iyyu sun sami ma'aikatu 6.

Wannan dai shi ne karon farko da ake samun gwamnatin hadaka a kasar Afirka ta Kudu wanda ya biyo bayan rashin samun rinjaye da jam'iyya mai mulki ta ANC ta yi a zaben da ya gabata.

Shugaba Cyril Ramaphosa a yayin jawabin kaddamar da sabuwar majalisar ministocinsa, ya bayyana cewa wannan gwamnatin za ta yi aiki cikin gaggawa don bunkasa tattalin arzikin kasar da ma samar da ayyuka ga matasa.
 

People are also reading