Home Back

'Sojoji za su ci gaba da tabbatar da tsaro a Kenya'

bbc.com 3 days ago
jami'an tsaron Kenya

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/SHUTTERSTOCK

Ministan tsaro na Kenya ya lashi takobin barin sojoji su ci gaba da sintiri a titunan kasar har sai al’amura sun koma daidai, an samu kwanciyar hankali, bayan mako guda na tarzomar siyasa.

Kasar na shirin fuskantar wata sabuwar zanga-zangar a makon da za a shiga, inda za a dora bayan wadda ta tilasta wa Shugaba William Ruto watsi da shirin gwamnatinsa na kara haraji.

Jim kadan bayan da wani alkali ya bayar da umarnin cewa kada jami’an tsaro su yi amfani da karfin da ya wuce kima a kan masu zanga-zanga, ministamn tsaron kasar ta Kenya, ya sanar da cewa za a baza sojoji domin su taimaka wa ‘yan sanda wadanda masu zanga-zanga suka rinjaya.

Adan Duale ya ce an dauki wannan matakin ne domin kalubalen tsaro da ake ciki a sanadiyyar zanga-zangar gama-gari da ta rikide ta zama tarzoma.

A bayaninta kungiyar kare hakkin dan’Adam ta duniya, ta Human Rights Watch, ta ce mutum akalla 30 aka kashe lokacin da ‘yan sanda suka bude wuta a kan masu zanga-zanga a cikin makon da ke karewa.

Kungiyar ta ce ‘yan sandan sun rika harbin hatta mutanen da ke tserewa daga zanga-zangar.

Matasa masu boren na bukatar ganin an cire, ayyukan da hukumomi suka kirkiro wadanda ba sa cikin tsarin mulkin kasar, da janye wasu haraje-haraje da korar jami’an gwamnati wadanda suka taba aikata wasu miyagun laifuka.

People are also reading