Home Back

Wata Sabuwa: EFCC Ta Buɗe Littafin Kwankwaso

leadership.ng 2024/7/6
Wata Sabuwa: EFCC Ta Buɗe Littafin Kwankwaso

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta fara bincike kan zargin karkatar da kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe da jam’iyyar NNPP ta yi a zaben 2023. Binciken dai ya mayar da hankali ne kan zarge-zargen da ake yi wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da tawagarsa, musamman gazawar kwamitin ayyuka na jam’iyyar a ƙarƙashin jagorancin Kwankwaso, wajen biyan wakilan jam’iyyar da suka yi aiki a lokacin zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna.

EFCC na bin diddigin ikirarin da Kwankwaso da sakatariyarsa, Misis Folashade Aliu, suka yi na karkatar da kuɗaɗen ta hanyar wani asusun kamfen na sirri da kuma bayar da tallafi.

Hukumar EFCC ta gayyaci Comrade Oginni Olaposi Sunday, sakataren jam’iyyar NNPP domin ya tabbatar da waɗannan zarge-zarge. A cewar wasu majiyoyi, koken Oginni ya shafi manyan masu sa hannun a asusun bankin NNPP da suka haɗa da Farfesa Rufa’i Alkali, Abba Kawu, da Dipo Olayokun.

EFCC na iya tsawaita bincikenta don bincikar Olayokun yadda ya tara dukiya da a Abuja cikin kankanin lokaci, wanda hakan ke nuni da cewa za a iya tafka maguɗi a harkar kuɗi da ke da nasaba da rawar da ya taka a matsayinsa na sa mai sa hannu.

Da yake tabbatar da ziyarar da ya kai shelƙwatar EFCC a kwanakin baya, Oginni ya bayyana cewa ya bayar da bayanan da suka dace da kuma ƙarin haske dangane da ƙarar.

Ya yabawa jami’an na EFCC bisa kwarewarsu tare da jaddada ƙudirin hukumar na yaki da cin hanci da rashawa. Yayin da Oginni ya tabbatar da binciken hukumar EFCC, ana sa ran nan ba da daɗewa ba za a gurfanar da Sanata Kwankwaso da sauran masu ruwa da tsaki kan zargin almundahanar Naira biliyan 2.5.

People are also reading