Home Back

Dalilan ƙwatar wa ƙananan hukumomi ‘yancin su daga hannun gwamnonin jihohi a Kotun Ƙoli

premiumtimesng.com 2024/8/25
ƘARIN ALBASHI: Bayan Tinubu ya ɗora Naira 2,000 kan Naira 60,000, Gwamnoni sun ce 60,000 ɗin ma ba za su iya biya ba

Kotun Ƙoli ta bai wa ƙananan hukumomin Najeriya 774 ‘yancin cin gashin kan su.

Yayin da ta ke karanto hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke, Babban Mai Shari’a Emmanual Agim ya ce Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin cewa haramun ne daga yau Alhamis gwamnoni su riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomi.

Mai Shari’a Agim ya ce an shafe shekaru sama da 20 kenan ana fama da gwamnonin jihohi su daina riƙe wa ƙananan hukumomi kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ke ba su, amma gwamnonin sun ƙi dainawa.

Ya ce tuni ƙananan hukumomi sun daina samun kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ke bai wa gwamnonin jihohi domin su ba su.

Yayin da ya ce daga yau ƙananan hukumomi ne za su riƙa kula da kuɗaɗen su tare da kashe su ta hanyar yin ayyuka kai-tsaye daga hannun su, Agum ya yi fatali da jayayyar da gwamnonin jihohin 36 suka yi, inda su ka ce Antoni Janar na Tarayya ba shi da ikon shigar da gwamnonin ƙara a Kotun Ƙoli.

Ya ce Antoni Janar na da ‘yancin shigar da ƙara a kotu.

“Daga yau kada Gwamnatin Tarayya ta ƙara tura wa ƙananan hukumomi kuɗaɗen su ta hannun gwamnonin jihohi.

Daga yau Gwamnatin Tarayya ta riƙa tura wa kowace ƙaramar hukuma kuɗaɗen ta kai-tsaye a asusun bankin ta, ba ta hannun gwamnonin jihohi ba.” Haka hukumcin na Kotun Ƙoli ya tabbatar.

Idan ba a manta ba, cikin watan Mayu ne Kotun Ƙoli ta nemi gwamnoni 36 su gabatar da bayanan dalilin da ba su so a ɓamɓare ƙananan hukumomi daga ƙarƙashin su.

A wancan lokacin, Kotun Ƙoli ta umarci gwamnonin Najeriya 36 kowa ya aika da bayanan kare kai daga ƙarar da Antoni Janar na Tarayya, Lateef Fagbemi ya shigar, inda ya nemi kotun ta bai wa ƙananan hukumomin Najeriya ‘yancin cin gashin kan su da mallakar da gwamnonin jihohi suka yi masu.

Alƙalan Kotun Ƙoli bakwai ne suka zartas da umarnin a ranar Alhamis ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Lawal Garba.

Kotun ta ce su kai bayanan kare kan su a cikin kwanaki biyar.

A ranar Alhamis ɗin ce dai aka fara zaman shari’ar.

Wannan jarida ta buga labarin cewa Gwamnatin Tarayya ta maka gwamnoni 36 Kotun Ƙoli, ta na so a bai wa ƙananan hukumomi cin gashin kan su.

Gwamnatin Tarayya ta maka gwamnonin Najeriya 36, inda ta ke roƙon kotu ta tirsasa ƙwatar wa ƙananan hukumomin ƙasar nan 774 cin gashin kan su, wato a riƙa ba su kuɗaɗen su kai-tsaye, ba tare da an bai wa jihohi su ba su ba.

Ofishin Antoni Janar kuma Ministan Harkokin Shari’a na Tarayya ne ya shigar da ƙarar a Kotun Ƙoli, ya na neman kotun ta bai wa ƙananan hukumomin cin gashin kan su.

A cikin ƙara mai lamba SC/CV/343/2024, gwamnatin tarayya na so Kotun Ƙoli ta haramta wa gwamnoni rushe zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi.

Haka kuma ta na so a riƙa tura wa kowace ƙaramar hukuma kuɗaɗen ta kai-tsaye, ba ta hannun gwnonin jiha na.

Antoni Janar kuma Ministan Shari’a Lateef Fagbemi na kuma so Kotun Ƙoli ta haramta wa gwamnoni naɗa shugabannin riƙon ƙananan hukumomi.

An dai shirya za a saurari ƙarar a ranar 30 ga Mayu.

An daɗe ana ƙorafin yadda gwamnonin jihohi ke sarrafa ƙananan hukumomi.

Ko kwanan nan tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, Farfesa Attahiru Jega ya ce zaɓen shugabanni ba shi da bambanci da taron naɗa basaraken gargajiya.

Dalilan Da Suka Sa Gwamnatin Tinubu Kwatar Wa Ƙananan Hukumomi ‘Yanci Daga Gwamnonin Jihohi – Akume, Barau Jibrin:

Cikin watan Mayu ne Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akune ya bayyana cewa Tinubu na goyon bayan bai wa ƙananan hukumomi cikakken ‘yancin cin gashin kai.

A lokacin, Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ta na goyon bayan a bai wa ƙananan hukumomi 774 na faɗin ƙasar nan ‘yancin cin gashin kan su, kai-tsaye daga asusun gwamnatin tarayya.

Akume ya bayyana haka lokacin da yake wa manema labarai jawabi bayan kammala taron Majalisar Zartaswa a ranar Laraba, a Abuja.

An yi taron domin tattauna cikar Gwamnatin Tinubu shekara ɗaya da kafuwa.

Akume ya ce Shugaba Tinubu ya maida hankali sosai wajen bin doka da oda da tsarin mulkin ƙasa tun da ya hau mulki.

Ya ce Tinubu ya yi alwashin ci gaba daga inda gwamnatin da ta gabata ta tsaya a ƙoƙarin ganin an bai wa ƙananan hukumomi cin gashin kan su.

“A batun nema da kiraye-kirayen a yi taron ƙasa don a tattauna batun cin gashin kan ƙananan hukumomi, ina ganin Majalisar Dattawa ta yi ƙoƙari sosai.”

“Wannan gwamnatin ita ma ta na goyon bayan wannan batu, kuma za mu ci gaba da ƙoƙarin ya tabbata a ƙasar nan.”

Ya ce wannan gwamnati ta yi amanna cewa ƙananan hukumomi sun fi sauran gwamnatocin tarayya da jihohi kusanci da jama’ar yankunan karkara.

Ya ce sai dai kuma duk da haka akwai gwamnonin jihohi waɗanda su ke da ‘yancin karɓar kuɗaɗe daga Asusun Gwamnatin Tarayya.

Makonni biyu da suka gabata ne dai Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin ya ce Gwamnoni sun kashe ƙananan hukumomi, su na karkatar da kuɗaɗen su ba bisa ƙa’idar doka ba.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya jaddada cewa gwamnoni na karkatar da kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ke bai wa ƙananan hukumomi suna sha’anin gaban kan su da kuɗaɗen.

Barau ya bayyana haka a ranar Laraba, yayin da ya shugabanci zaman majalisar dattawa.

Ya furta haka ne bayan Sanata Kawu Sumaila na NNPP daga Kano ya kawo ƙorafin buƙatar a bai wa kowace ƙaramar hukuma cin gashin kanta.

Sanata Jibrin ya ce tabbas wasu gwamnoni su na ƙananan hukumomi illa sosai, saboda son zuciyar su.

Ya ce gwamnoni su na kamfatar kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya ke bai wa ƙananan hukumomi, lamarin da Barau ya ce zamba ce.

“Tsarin ƙananan hukumomi ya mutu murus, saboda kuɗaɗen da tarayya ke ba su, akasari duk gwamnoni ke karkatar da su.

“Za a ce ku je ku rubuto kuɗaɗen da ku ke buƙata, daga nan sai gwamna ya daddatsa kuɗaɗen ya kamfaci iya son ran sa.”

Amma fa ban ce haka dukkan gwamnoni ke yi ba. Akwai gwamnoni mutanen kirki, waɗanda ba su yin hakan. Amma wasu da na aikata hakan.” Cewar Barau.

Ya ce hanyar da za a iya bai wa ƙananan hukumomi cin gashin kan su. Hakan kuwa ba zai yiwu ba sai an shigar da dokar cikin Kundin Dokokin Najeriya.

Daga nan ya jinjina wa gwamnonin da ba su cirar kuɗaɗe daga asusun ƙananan hukumomi, sannan ya yi kira gwamnonin da ke cirar kuɗaɗen su daina.

People are also reading