Yajin Aiki: Kungiyoyin Kwadago Sun Kulle Majalisar Tarayya a Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Kungiyar ma’aikatan majalisar tarayyar Najeriya (PASAN) sun tsunduma cikin yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago suka fara a faɗin Najeriya.
Ma'aikatan ƙungiyar sun kulle majalisar tarayya domin bin umarnin ƙungiyoyin ƙwadago na shiga cikin yajin aikin.
Ƙungiyar ta rufe ƙofofi biyu na harabar majalisar inda ma’aikata da sauran masu son zuwa majalisar suka kasa samun damar shiga, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƙungiyar ta kuma datse wutar lantarki da ruwan sha ga gine-gine biyu na majalisar dattawa da ta wakilai da kuma sauran ofisoshi a harabar.
Wasu ma’aikatan agaji a harabar da suka je bakin aiki ba su samu damar shiga ba, yayin da aka ga jami’an ƙungiyar na ɗaukar matakin tabbatar da ana yin yajin aikin.
Yajin aikin ya shafi sakatariyar gwamnatin tarayya, inda akwai ofisoshin ma'aikatun ƙwadago da samar da ayyukan yi, sadarwa, Neja Delta da sauransu.
A sakatariyar an ga shugabannin ƙungiyoyin na shige da fice domin tabbatar da cewa babu ma'aikacin da ke aiki a ofis.
A wani labarin kuma, kun ji cewa yajin aikin ƙungiyoyin ƙwadago na Najeriya NLC da TUC na ci gaba da ɗaukar zafi a babban birnin tarayya Abuja.
Ƙungiyoyin ƙwadago sun rufe babbar kofar ma'aikatar babban birnin tarayya Abuja wadda aka fi sani da kofar Minista, inda a ka hana ma’aikatan shiga.
Asali: Legit.ng