Home Back

Philippines Ta Zama Makamin Sarrafawa Ga Amurka

leadership.ng 6 days ago
Philippines Ta Zama Makamin Sarrafawa Ga Amurka

A yanzu haka a yankin kudu maso gabashin Asiya, kasar Philippines ta fi zama abokiyar huldar kud da kud da kasar Amurka. Amma kila kalaman tsoffin jami’an wasu kasashe dangane da huldar ta da Amurka, abubuwan takaici ne gare ta. Sun kuma ba wa ‘yan siyasan Philippines marasa wayo darasi.

Tsohon firaministan kasar Malaysia Mahathir Mohamad ya bayyana a kwanan baya, yayin da yake hira da manema labaru cewa, Amurka ba ta yankin tekun kudancin kasar Sin, amma ga alama tana sha’awar tunzurawa a yi fito-na-fito tsakanin kasashe, har ma ta taimaka musu yin yaki da juna, kamar yadda al’amari yake gudana a tsakanin kasashen Ukraine da Rasha. Idan yaki ya barke, Amurka ta kan sayar da makamai masu yawa. Ban da haka kuma, tsohon dan majalisar dattawan Amurka, kuma tsohon kanar Richard Black, ya tunatar da Philippines bukatar ta kai zuciya nesa, ta kimanta halin da take ciki, a kokarin kauracewa zama makamin sarrafawa na Amurka, da kuma shiga rikicin makamai sakamakon tunzurawar da sojan Amurka suke yi mata. A karshe dai, za a haifar da barna ga jama’ar Philippines.

Kamar yadda tsoffin jami’an Amurka suka fada, ainihin makasudin manufofin jakadancin Amurka, shi ne kiyaye zama madaukakiya a yankin Asiya da tekun Pacific da ma baki dayan duniya, don haka tana dakilewa, da danne wadanda a ganinta za su kabulance ta a nan gaba. Ma iya cewa, dalilin da ya sa Amurka ta sa hannu a harkokin tekun kudancin kasar Sin, shi ne mayar da Philippines matsayin makamin amfani na dakile ci gaban kasar Sin, a maimakon kiyaye kawance a tsakaninta da Philippines, ko kuma abokantaka a tsakaninta da Philippines. Ba shakka Amurka za ta jefar da Philippines, da zarar ta gama amfanin da ita. (Tasallah Yuan)

People are also reading