Home Back

Manoman citta a jihohi uku da Abuja sun samu tallafin naira biliyan 1.6 daga gwamnatin Tarayya

premiumtimesng.com 2024/5/19
Manoman citta a jihohi uku da Abuja sun samu tallafin naira biliyan 1.6 daga gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta ware naira biliyan 1.6 domin tallafa wa manoman noman citta a jihohin uku da Babban Birnin Tarayya Abuja.

Babban sakataren asusun bunƙasa noman citta ta kasa NADF Mohammed Ibrahim ya sanar da haka a wani taro da ya yi a Kaduna a cikin makon jiya.

Gwamnati za ta raba wannan tallafi a karkashin Shirin bynƙasa noma na ‘GRATE’.

Ibrahim ya ce akalla manoman cirta 15,000 ne cutar ‘Blight’ ya shafa a jihohin Kaduna, Filato, Nasarawa da Abuja a Kuma lokacin da kasar ke bukatan citta domin siyarwa a kasashen waje.

Sakamakon bincike da NBS ta gabatar ya nuna cewa Najeriya ta samu kari a kudaden shiga a dalilin kasuwancin citta zuwa kasashen waje daga naira biliyan 4.6 a 2022 zuwa naira biliyan 10 a 2023.

Ibrahim ya ce tallafin da gwamnati ta bada za a yi amfani da su ne wajen Samar wa manoma ingantattun iri, maganin feshi da takin zamani.

Ya ce suna sa ran cewa tallafin da gwamnati ta bada zai taimaka wajen bunƙasa noman a kasar nan.

People are also reading