Home Back

Gaza: Yara da mata na sumewa saboda rashin abinci

bbc.com 2024/7/3
Abdulaziz mai wata biyar da haihuwa na fama da rashin abinci mai gina jiki a Gaza mother, who is dressed in a black abaya
Bayanan hoto, Abdulaziz na da nauyin kilo uku ne kacal kuma ba a daɗe da fito da shi daga ɗakin marasa lafiya da ke neman kulawa ta musamman ba
  • Marubuci, Adnan El-Bursh
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC Arabic a Gaza
  • Aiko rahoto daga Doha

Abdulaziz al-Hourani, jariri ne ɗan wata biyar, yana kwance a asibitin Al-Ahli da ke arewacin Gaza, ramammen jikinsa na nuna cewa yana fama da rashin isasshen abinci.

Nauyinsa kilo uku ne kacal, ba a daɗe da fito da shi daga ɗakin masu neman kyulawa ta musamman ba inda ake kula da saboda yana fama da karancin abinci.

Mahaifiyarsa ta ce ba ya iya samun abincin da yake buƙata a yankin na Gaza. "Wannan ne ɗana ɗaya tal, ya kamata a ce yanzu nauyinsa ya kai kilo biyar, ina matuƙar jin tsoro saboda lafiyarsa," in ji ta. "Ba na iya kai shi wata ƙasa saboda an rufe iyakoki."

Akwai labarai irin na Abdulaziz bila-adadin a yanki. Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce sama da yara 8,000 ƴan ƙasa da shekara biyar na fama da matsananciyar yunwa tun bayan da yaƙi ya ɓarke - daga cikin yaran, guda 1,600 na cikin mummunan hali.

A makon da ya gabata, shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Adhanom Ghebreyesus ya ce "mutum 32 ne ake kyautata zaton yunwa ta kashe, 28 daga cikin su yara ne ƴan ƙasa da shekara biyar".

A farkon watan Yuni, Hukumar yara ta Majalisar Dinkin Duniya (Unicef) ta ruwaito cewa yara 9 cikin 10 a Gaza na fama da ƙarncin abinci, inda suke samun nau'ukan abinci masu gina jiki guda biyu kacal a rana.

Ta ƙara da cewa "watannin da aka kwashe ana artabu da hana shigar da kayan tallafi sun dagula harkar samar da abinci da na kiwon lafiya, wani abu da ya haifar da mummunan yanayi" kuma ƙananan yara "na cikin mummunar yanayin rashin abinci wanda ke barazana ga rayuwarsu".

Ana ciyar da Abdulaziz mai wata bakwai ta hanyar amfani da sirinji
Bayanan hoto, Mahaifiyar Abdulaziz ta ce ba su iya samun abincin da ya dace a Gaza

Babu komai a kasuwanni

An haife ni ne a Gaza, kuma a nan na girma tare da iyalina - ina ta aiko rahotanni daga can har zuwa watan Fabarairu.

Kafin ɓarkewar yaƙi, yankin al-Tufah na Gaza wuri ne mai cike da hada-hadar kasuwanci, to amma yanzu idan na kira mutanen da har yanzu ke rayuwa a can suna turo min hotunan wurin, wanda a yanzu ya zama tamkar babu kowa.

Salim Shabaka, wani dattijo a kasuwar ya ce: "Babu tumatur, babu gurji babu kayan itatuwa kuma babu burodi."

Ya faɗa min cewa babu sauran kayan a zo a gani, sai gwanjo ƙalilan da kuma kayan gwangwani ƙalilan waɗanda suka rage.

"Ba mu taɓa shiga rayuwa irin wannan ba - babu abin saye ko na sayarwa." in ji ɗan kasuwan.

"Akwai yara waɗanda ba su samu taimako ba."

A kowace rana mutane kan yi dogayen layi a ƙananan kantunan da ake bayar da abinci kyauta.

Mafi yawan lokuta masu hannu da shuni a arewacin Gaza ne ke ɗaukar nauyin raba abincin, to amma ƙarancin hakan na nufi akwai barazana a gaba.

Amma a halin yanzu irin waɗannan wurare ne kawai yara ke zuwa domin samun abincin da aka dafa, yayin da wasu ke tafiya mai nisa domin nemo ruwa.

Kasuwar al-Tufah da ke arewacin Gaza, wadda a baya ta kasance cibiyar hada-hadar kasuwanci, yanzu ta zama tamkar kufai
Bayanan hoto, Kasuwar al-Tufah da ke arewacin Gaza, wadda a baya ta kasance cibiyar hada-hadar kasuwanci, yanzu ta zama tamkar kufai

Yunwa da cututtuka

Kusan kowace rana nakan yi waya da ƴan'uwa da abokaina da ke a Gaza. A cikin hotunansu da suke turo min, zan iya ganin sun rame kuma fuskokinsu sun canza.

Kuma shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya yi gargaɗin cewa "har yanzu babu alamar cewa waɗanda ke cikin matsananciyar buƙatar abinci na samunsa duk kuwa da ƙarin kayan agaji da ake shigarwa."

Ya ƙara da cewa wuraren kula da masu fama da matsalar ƙarancin abinci guda biyu ne kacal ake iya samarwa sanadiyyar rashin tsaro.

Ya yi gargaɗin cewa rashin hanyoyin kiwon lafiya da rashin ruwa mai tsafta da rashin tsaftar muhalli "na ƙara haɗarin da yara masu fama da ƙarancin abinci ke ciki."

Yanayin na nuna cewa za a iya shiga haɗarin yaɗuwar cutuka kamar na hanta. An rufe yawancin asibitoci yayin da waɗanda suka saura suna aiki na fama da cunkoso sannan an lalata wasu ɓangarorinsu.

"Mun galabaita, ba mu da sauran ƙarfi," in ji Umm Fouad Jabeer, wata dattijuwa da ke a Jabaliya a arewacin Gaza. "An kore mu daga matsugunanmu babu adadi kuma a kullum ana kashe mutane.

"Mun ci abincin dabbobi, yara da mata na sumewa sanadiyyar yunwa. Cutuka sun addabe."

Wani likita a yankin Falasɗinawa, Moatasem Saed Salah, wanda ke cikin kwamitin agajin gaggawa na ma'aikatar lafiya ta Hamas, ya tabbatar da cewa a kullum ana samun gomman mutane, musamman yara da mata masu ciki da masu shayarwa, waɗanda ke fama da cutar yunwa.

Ya ce wasu cututtukan na ƙara kama mutanen da dama suna fama da wata rashin lafiyar ta daban.

Matsalar kai agaji

Yaƙin ya ɓarke ne bayan da mayaƙan ƙungiyar Hamas suka ƙaddamar da hari kan Isra'ila a ranar 7 ga watan Okotoba, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutum 1,200 da kuma yin garkuwa da wasu 251 a Gaza.

Ma'ikatar lafiya da ke ƙarƙashin Hamas ta ce sama da Falasɗinawa 37,000 ne aka kashe tun bayan ɓarkewar yaƙin, yayin da aka raunata tare da tarwatsa wasu dubbai.

Al'ummar Gaza sun dogara ne da taimakon da za a kawo daga waje, sai dai ba a samun damar shigar da isasshen tallafi.

Dogon layin karɓar abinci a gaban rumfunan da ake raba abinci kyauta a Gaza
Bayanan hoto, Dogon layin karɓar abinci a gaban rumfunan da ake raba abinci kyauta a Gaza

A baya, mashigar Rafah da ke kan iyakar Gaza da Masar ta kasance babbar hanyar shigar da agaji zuwa Gaza, amma yanzu an rufe ta bayan da Isra'ila ta ƙwace iko da mashigar.

Sai kuma ta ɓangaren kudu inda ake da mashigar Kerem Shalom wadda ta haɗa da Isra'ila, tana buɗe amma faɗan da ake gwabzawa ya hana a riƙa shigar da kayan agaji yadda ya kamata.

Sai dai akan samu damar shigar da kayan abinci ta wasu sabbin mashigai da ke ɓangaren arewaci, sai dai yawan abincin da ake shigarwa ya yi ƙasa da kimanin kashi biyu cikin uku daga ranar 7 ga watan Mayu.

A makon da ya gabata, hukumomin Hamas a Gaza sun bayar da rahoton cewa kimanin manyan motoci 35 ne ke shiga Gaza a kowace rana, kuma su ne kaɗai hanyar samun abinci da magunguna ga mutum 700,000 da ke zaune a arewacin Gaza.

Amma a wani bayani da ta wallafa a shafin X, hukumar tsara ayyukan agaji ta Isra'ila (Cogat) ta ce: "abinci wanda darajarsa ta kai na kuɗi fan biliyan ɗaya ne aka tura zuwa Gaza tun bayan ɓarkewar yaƙin."

People are also reading