Tirela Ta Yi Gaba da Gaba da Karamar Mota, Ta Markaɗe Mutane Har Lahira
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Keffi, Nasarawa - An samu mummunan hadari tsakanin wata mota kirar Honda Accord da babbar mota kirar tirela.
Rahotanni sun nuna cewa motocin sun yi karo da juna ne wanda hakan ya jawo mutuwar mutane da jikkata da dama.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa hadarin ya faru ne a lokacin da babbar motar ta nufi hanyar Keffi daga Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa hadarin ya faru ne sakamakon tsinkewar birkin babbar motar.
Waɗanda suke wurin sun tabbatar da cewa matukin babbar motar ya gagara riketa yayin da yake gangarowa daga tudun Kugbo da ke kan hanyar Abuja zuwa Keffi.
Rahotanni sun nuna cewa tirelar ta markaɗa mutane hudu da ke cikin karamar motar har lahira ta yadda aka gagara gane su.
An kuma ruwaito cewa sauran mutanen da haɗarin ya ritsa dasu sun samu munanan raunuka a wurare da dama, rahoton Daily Post.
Biyo bayan haɗarin, jami'an hukumar kiyaye hadura ta kasa (FRSC) sun isa wajen cikin gaggawa domin mika agaji.
Jami'an sun yi kokarin ciro bangarorin mutanen da matar ta markaɗa domin a samu damar musu janaza.
A wani rahoton, kun ji cewa hukuma mai kula da haɗura ta ƙasa (FRSC) ta fitar da rahoto kan yadda bikin sallah ya gudana a wasu jihohin kudancin Najeriya.
Rahoton da hukumar FRSC ta fitar ya nuna cewa an samu haduran mota da dama wanda ya jawo asarar rayuka da jikkata mutane da yawa.
Asali: Legit.ng