Home Back

YAJIN AIKI: NLC da TUC sun katse wutar Najeriya baki ɗaya

premiumtimesng.com 2024/7/6
Lantern light
Lantern light

Yayin da ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC suka tsunduma yajin aikin neman ƙarin albashi, Hukumar Wutar Lantarki ta Najeriya ta bayyana cewa masu yajin aiki sun kulle babbar tashar bayar da wutar lantarki, lamarin da ya jefa ƙasar nan cikin duhu baki ɗaya.

Babbar Manajar Hulɗa da Jama’a da Yaɗa Labarai ta hukumar TUC, Ndidi Mbah, ta ce an jefa Najeriya cikin duhu daidai ƙarfe 2:19 na daren wayewar safiyar Litinin.

“Hukumar Wutar Lantarki ta Ƙasa na sanar da cewa ƙungiyoyin ƙwadago sun katse wutar lantarkin Najeriya baki ɗaya. Hakan ya na nufin sun jefa Najeriya cikin duhu, tun daga ƙarfe 2:19 na dare, 3 ga Yuni, 2024.” Cewar Ndidi.

‘Cikin Talatainin Dare Masu Zanga-zanga Suka Jibgi Ma’aikatar Rarraba Wutar Lantarki’ – TCN

“Wajen ƙarfe 1:15 na dare, hasalallun ma’aikata a Tashar Lantarki ta Benin sun fatattaki waɗanda ke kan aikin rarraba wuta a daren. Waɗanda suka nuna rashin goyon bayan katse wutar kuma aka yi masu dukan tsiya, har aka raunata wasu.”

Sauran ƙananan tashoshin bada wutar lantarki da aka katse sun haɗa da ta Ganmo, Benin, Ayede, Olorunsogo, Akangba da Osogbo.

Sai dai ta ce an kashe babban inji ɗaya a tashar wutar lantarki ta Jebba, aka bar sauran tashoshi uku.

“Wajen ƙarfe 3:23 TUC suka fara aikin gaganiyar dawo da wutar, ta hanyar amfani da tashar wutar lantarki ta Shiroro, domin samar da wuta a tashar wutar lantarki da ke Katamfe,”.

Ta ce TCN zai ci gaba da aikin dawo da wutar a faɗin ƙasar nan.

People are also reading