Home Back

Gwamnan Kano Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Kawo Karshen Fadan Daba A Kano

leadership.ng 2024/7/2
Gwamnan Kano Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Kawo Karshen Fadan Daba A Kano

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a ranar Asabar ya bai wa jami’an tsaro umarnin su gaggauta dakile matsalar fadan daba da sauran ayyukan bata gari wanda ke gurgunta zaman lafiya a wasu sassan Jihar.

‘Yan daba a cikin kwanaki biyu sun mayar da  kwaryar birnin Kano wuri mara tabbas ta fuskar rahotonnin fadace-fadace, kwace kwayoyin hannu da sauran kananan Laifuka.

Gwamnan ya bayar da wannan umarni ne  a lokacin taron mako-mako na majalisar zartarwar da aka gudanar a dakin taron fadar Gwamnatin Kano.

Gwamnan Abba Kabir Yusuf ya bayyana damuwarsa kan  yawaitar bullar fadace-fadacen daba, inda ya tabbatar da cewa Gwamnati ba za ta zuba ido ana kallon wadannan ayyukan daban, na ci gaba da tada  hankulan jama’a tare da haramtawa tarin jama’a masu kokarin kiyaye doka ci gaba da samun kwanciyar hankali ba.

Ya Jaddada cewa Gwamnatin Kano  za ta ci gaba da hada hannu da hukumomin tsaro domin tabbatar  da kiyaye rayukan da dukiyoyin  al’umma a ko wane lokaci.

Kazalik, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bukaci alkalai da su guji sakin ‘yan daba, inda ya jadadda barazanar da hakan ke haifarwa ga  kwanciyar hankalin mazauna Kano, sannan ya bayyana muhimmancin gaggauta yanke hukunci kan wadanda ke gaban shari’a.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bai wa hukumomin tsaro umarnin  da su tabbatar da yin aiki kamar yadda doka ta tsara wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma da suke yi wa aiki, ya ja kunnensu da su tsaya iyakar da doka ta tsara musu.

A karshe Gwamnan ya bukaci jama’ar Kano da su ci gaba da gudanar da harkokinsu, inda ya ba su tabbacin Gwamnati za ta kara jajircewa wajen tabbatar da tsaro tare da bukatar ci gaba da bai wa wannan Gwamnati cikakken hadin kai da goyon baya.

People are also reading