Home Back

Legas ta ƙwace baburan ‘yan acaɓa 359, bayan an markaɗe matsugunan ‘yan share-wuri-zauna

premiumtimesng.com 2024/5/12
Legas ta ƙwace baburan ‘yan acaɓa 359, bayan an markaɗe matsugunan ‘yan share-wuri-zauna

Gwamnatin Jihar Legas ta sake ƙwace baburan ‘yan acaɓa har 359, waɗanda ke kabu-kabu a bakin mayanka dabbobi da kuma gefen titin jirgin ƙasa.

Haka kuma an murtsike wuraren kwanan ‘yan share-wuri-zauna, domin a ƙara haskakawa da tsaftace wuraren.

Hukumar Tsaftace Legas daTilasta da Tirsasa Bin Dokoki ta bayyana haka a ranar Laraba, ta ce wuraren da aka ruguje duk bukkoki ne da masu kwana waje suka kakkafa saboda kunnen ƙashin kangare wa dokar hukuma.

Hukumar ta ce kuma an ƙwace babura ne saboda ana zirga-zirgar ɗaukar fasinja a daidai hanyar titin jirgin ƙasa.

Kakakin rundunar kamen babura mai suna Gbadeyan Abdulraheem ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya aiko wa PREMIUM TIMES, ya ce an rushe ɗakunan ne a Fagba.

Gagarimin aikin rusau da ƙwace baburan sai ya ɗauki kwanaki biyu ana gudanar da shi, bayan ƙaddamar da aikin titin jirgin ƙasa a jihar.

Shugaban hukumar, Shola Jejeloye ne da kan sa ya jagoranci aikin rusau ɗin a Fagba, Iju-Ishaga, Mayanka da Pen Cinema, inda aka ƙwace babura masu ɗimbin yawa.

Jejeloye ya ce ‘yan dabar da ke sagarabtu a mayanka sun haɗa kai da masu baburan su na hana jami’an su aikin ƙwace baburan, amma duk da haka an yi nasarar ƙwace babura 359.

People are also reading