Home Back

IPMAN Ta Yi Barazanar Rufe Gidajen Mai Sama Da 30,000 Saboda Bashi

leadership.ng 2024/5/17
IPMAN Ta Yi Barazanar Rufe Gidajen Mai Sama Da 30,000 Saboda Bashi

Kungiyar dillalan man fetur ta Nijeriya (IPMAN), ta ayyana cewar za ta rufe gidajen mai 30,000 matukar gwamnatin tarayya ta gaza biyan bashin Naira biliyan 200 da ta ke binta.

Ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwar bayan taro da shugaban kungiyar mamallaka rumbunan adana man fetur, Yahaya Alhassan ya fitar a Abuja.

Leadership ta ruwaito cewar, hukumar da ke kula da kasuwancin albarkatun man fetur ta Nijeriya (NMDPRA) wacce mallakin gwamnatin tarayya ce, ta gaza biyan bashin, wanda ya ci gaba da taruwa tun cikin watan Satumbar 2022.

IPMAN na da iko da fiye da gidajen mai 30,000 a fadin Nijeriya.

Hakkokin tura mai wasu kudade ne da gwamnati ke biyan dillalan mai saboda safarar albarkatun man fetur din da aka loda daga rumbunan adana man zuwa jihohin da ke fadin kasar nan.

A cewar Alhassan, sakamakon gaza biyan bashin Naira biliyan 200 daga bangaren NMDPRA ba zai zamo mai kyau ba.

Alhassan ya kara da cewar, “a matsayinmu na IPMAN, mun dauki dukkanin matakai a ba ya domin kauce wa fadawa cikin wannan mummunan al’amari, wanda muka tabbatar ba zai yi wa ‘yan Nijeriya dadi ba.

“Amma yanzu ba mu da wani zabi illa mu fito kwanmu da kwarkwata domin magance wannan matsala ta hanyar da muka fi ganin ta dace, wanda hakan ka iya sake ‘yan Nijeriya cikin halin kunci da wahala.”

People are also reading