Home Back

Mun Fara Aiki Da ‘Yan Bori – Hukumar Tace – Fina-finai

leadership.ng 2024/7/6
Mun Fara Aiki Da ‘Yan Bori – Hukumar Tace – Fina-finai

Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano, ta sanar da shirinta na hada kai da kungiyar ’yan bori, wadanda aka fi sani da masu aiki da aljanu.

Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, ya ce hukumar za ta yi aiki da ’yan borin ne, da zummar tsaftace ayyukansu ta yadda za su yi daidai da doka.

Sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar a ranar Talata, ta ruwaito cewa Abba El-Mustapha ya sanar da haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar ’yan bori ta Jihar Kano a ofishinsa.

El-mustapha, ya nemi hadin kai tare da cikakken kungiyar ’yan borin ta yadda a cewarsa, za a gudu tare a tsira tare.

A jawabinsa a madadin kungiyar, shugaban majalisar ’yan bori masu aiki da aljanu na karamar Hukumar kumbotso, Malam Sabo Isyaku Wailari cewa ya yi, sun ziyarci hukumar ne domin kulla alaka.

A cewarsa, bangaren ya hada da tallata maganin gargajiya domin su tabbatar da ’ya’yan kungiyar suna amfani da kalmomin da ba su saba dokokin hukumar ba.

Ya kara da cewa kungiyar tana yin iya kokarinta wajen tabbatar da cewa mambobinta ba su yin wasa a lokacin da ya ci karo da lokacin sallah ba, ko a kusa da Masallatai, makabartu ko makarantu.

A karshe ya yi wa hukumar alkawarin cewa kungiyarsu za ta ci gaba da bai wa hukumar cikakken hadin kai tare da goyon baya.

People are also reading