Home Back

INEC Ta Yi Wa Jam’iyyun Siyasa Gori A Kan Rajistar Mambobi

leadership.ng 2024/7/6
INEC Ta Yi Wa  Jam’iyyun  Siyasa Gori A  Kan Rajistar  Mambobi

Hukumar zave mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa babu wata jam’iyyar siyasa a Nijeriya da ta kammala yi wa mambobinta rajista. Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu shi ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a garin Benin.

Yakubu ya kalubalanci jam’iyyun siyasa su kammala yi wa mambobinsu rajista idan har suna so hukumar ta yi musu dukkan abun da suke bukata. Ya ce INEC ta fi su yawan mutane, wanda take da yawan masu rajistar zave da suka miliyan 93, kuma duk sun kamala rajistarsu. Ya ce, “Kamar yadda a yau INEC ke da mafi girman bayanai na ‘yan Nijeriya da suka kai miliyan 93, wadanda suka kamala yin rajistar zave.

Har yanzu muna jiran jam’iyyun siyasa su ba mu cikakkun bayanan rajistar mambobinsu ko da a unguwa daya ne. “Babu wata jam’iyyar siyasa da ke da cikakken rajistar mambobinta ko da a unguwa daya. Amma idan sun zo taro irin wannan, za su rika kiranmu mu yi

musu abubuwan da suke bukata. “Wata gudunmawa kuka bayar matsayinku na jam’iyyan siyasa domin inganta tsarin dimokuradiyyarmu? Idan akwai jam’iyyar da ke da cikakken rajistar mambobinta a Jihar Edo ta daga hannu. Sannan zan kawo bayanan da kuka mika wa INEC in tabbatar da cewa ba gaskiya suke fadi ba. “Akwai lokacin da muka ce a kawo muna duk bayanan Abuja.

Sai wasu jam’iyyu suka fara cewa muna kai bayanan rajista daga unguwa zuwa Abuja yana da wuya. Amma ba gaskiya ba ne, saboda ba su kamala ba.”

Yakubu ya kara da cewa ana ci gaba da yin rajistar masu zave don bai wa wadanda ba su da katin zave damar yin rajistar zave da wadanda nasu ya vace da kuma wadanda suke bukatar sauya wurin yin zave.

Yayin da yake nuna rashin amincewa da ikirari da ake yi na cewa matasan sun rasa kwarin gwiwa daga wurin hukumar sakamakon zaven 2023 da aka gudanar, ya bayyana cewa mafi yawan wadanda a halin yanzu ke yin rajistar zave a jihohin Edo da Ondo matasa ne wanda shekarunsu yake tsakanin 18 zuwa 34. Ya ce lallai bai yarda matasa sun rasa kwarin kwiwa ga hukumar zave ba, domin suke yin tururuwan yin rajistar zave.

People are also reading