Home Back

Lamunin Naira Biliyan 5 Ga ‘Yan Fim: Yaushe Kannywood Za Ta Samu Nata?

leadership.ng 2024/10/5
kannywood

A tsakiyar makon da ya gabata ne aka samu labarin cewa gwamnatin tarayya ta bayar da karin wani kaso daga tallafin naira biliyan 5 ga masana’antar Nollywood, wanda labarin ya karade kafofin yada labarai a kasar nan.

Gwamnatin tarayyar ta ce wannan shi ne rukuni na biyu da ta bayar da irin wannan tallafi ga masana’antar Nollywood da ke shirya fina-finai da harshen Turanci a Nijeriya.

Gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar bankin Probidus sun bayar da kaso na biyu na kudaden da aka ware domin bunkasa harkokin masana’antun nishadi a Nijeriya, wanda kudin ya kai naira biliyan 5. An kafa wannan asusu ne a watan Disambar 2023, domin tallafawa da kuma bunkasa fannin kirkire-kirkire a Nijeriya.

Mataimaki na musamman ga ofishin mataimakin shugaban kasa kan fasahar tattalin arzikin zamani, Fegho Umunubo, ya sanar da labarin a cikin wani sakonsa a kafar sada zumanta ta ‘Instagram’ da ya wallafa.
Ya ce karkashin sabon tsarin sabunta fata na Shugaba kasa, Bola Ahmed Tinubu, “Mun yi nasarar kaddamar da kashi na biyu na susun tallafa wa masana’antar kirkire-kirkire ta Nijeriya da naira biliyan 5 tare da hadin gwiwar bankin Probidus da kuma otel din Eko Hotels and Suites a ranar Juma’ar da ta gabata.

“Bayan nasarar raba naira biliyan 1.5 ga ’yan wasa hudu da masu shirya fina-finai a masana’antar Nollywood, har yanzu kofa a bude take ga duk masu bukatar tallafi domin bunkasa harkokinsu na nishadi da kirkire-kirkire,” ya rubuta.

A watan Mayu na wannan shekarar aka raba kason farko na naira biliyan 1.5 ga jarumai da masu shirya fina-finai hudu.

Sai dai Fegho ya ce kudaden ba kyauta ba ne, domin ana sa ran wadanda suka amfana za su mayar da kashi 30 cikin 100 na kudaden da suka samu zuwa bankin Probidus a dan kankanin lokaci.

Hakan ya sa mutane da dama suke sha’awar ganin takwarar masana’antar Nollywood, wadda take shirya fina-finanta da harshen Hausa wato Kannywood ita ma ta samu kwatankwacin irin wannan tallafin, duba da cewa a lokuta da dama kamar dai Nollywood ita ma masana’antar Kannywood takan rasa wasu kudaden da za ta gudanar da wani abu wanda zai janyo mata ci gaba ya kuma daukaka sunan Nijeriya a idon duniya.

People are also reading