Home Back

'Yan Najeriya miliyan 18 na cikin tsananin yunwa

rfi.fr 2024/4/27
Dandazon masu saye da karanta jarida
Dandazon masu saye da karanta jarida AFP - EDUARDO SOTERAS

Jaridar leadership da ake wallafawa a Najeriya ta rawaito cewa masu ruwa da tsaki a bangaren noma a kasar sun ci gaba da bayyana damuwarsu a kan yadda ake garkuwa da manoma, abin da ke illa ga bangaren samar da abinci a kasar.

Wani bincike da jaridar leadership ta gudnar na nuna yawan 'yan Najeriya da ke fama da matsalar rashin abinci tsakanin rubu'in farko na shekarar bara zuwa rubu'in farko na bana, ya karu daga miliyan 66 da dubu 200 zuwa miliyan 100.

Binciken ya kuma ce, daga  cikinsu, akalla mutane miliyan 18 da dubu 600 ke fama da matsananciyar yunwa.

Kamaru ta rage farashin man fetur saboda tsadar rayuwa

A Jamhuriyar Kamaru jaridar Actu Kamaru ta ruwaito Ministan Kasuwanci Mr Luc Magloire Mbarga Atangana ya yi wa alummar kasar albishir na rage firashin mai, la’akari da yanayin tsadar rayuwa da suka tsinci kansu a ciki, sakamakon yadda ita kanta Kamaru din kamar sauran kasashe makota ta fuskanci matsalar matsin tattalin arziki.

Jaridar ta ce daga ranar 28 ga wannan watan ne sabon farashin zai fara aiki, inda za a rika siyar da kowacce jarka mai daukar lita 25 na mai kan CEFA dubu 27,700 sabanin CEFA dubu 30,000.

Wannan ne karo na 2 da aka samu ragin firashin mai a Kamaru daga tsakanin watan Disamban shekarar bara.

Sinawa sun mutu a wani harin kunar-bakin-wake

Global Times da ake wallafawa a China ta rawaito wani harin kunar bakin wake ya yi sanadiyar mutuwar akalla Sinawa 5 da direbansu dan asalin Pakistan a birnin Besham da ke yankin Arewa maso yammacin lardin Khyber Pakhtunkhwa.

Kamar yadda jaridar ta ruwaito lamarin ya faru ne a jiya Talata lokacin da dan kunar bakin waken ya yi taho mu gama da ayarin motocin ma’aikatan, bayan sun kama hanya daga Islamabad zuwa Dasu, madatsar ruwan da wani kamfanin China ke samar da wutar lantarki, mai nisan kilomita 270 daga babban birnin kasar.

Jaridar ta kara da cewa masu aikin ceto sun yi nasarar samo gawarwakin mutane 4 daga cikinsu, wasu biyu kuma sun kone kurmus, yayin da suke kan neman sauran mutane 2, kamar yadda kakakin hukumar agajin gaggawa na lardin Khyber Bilal Faizi ya shaidawa manema labarai.

Wani harin sama ya kashe mutane a Syria

Jaridar Observer ta Syria ta dauko labarin da ke cewa akalla mutane 8 aka kashe a wani harin sama a gabashin kasar, daga cikinsu akwai wani ma’aikacin Hukumar Lafiya ta Duniya hade da mashawarci kan harkokin tsaro a Iran.

Haka ma kafofin yada labaran kasar da suka yi sharhi a kan harin sun ce wadanda suka mutu sun hada da sojoji 7 da farar hula 1, kuma akalla wasu sojoji na daban 13 da fararen hula 19 suka jikkata a harin. Baya ga haka ya zuwa jiya talata ba a tabbatar da wadanda ke da alhakin kai harin ba.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce, jami’inta Emad Shehab da ya kasance injiniya a lardin Deir ez-Zor da ke kula da samar da tsaftataccen ruwan sha da tsaftar muhalli, ya gamu da ajalinsa ne lokacin da hare-haren sama suka farwa gininsa.

 
People are also reading