Home Back

Shinkafi Ya Fadi Abin da Ke Kawo Rashin Tsaro a Arewa Maso Yamma, Ya Ba da Mafita

legit.ng 2024/10/5
  • Kungiyar PAPSD ta nemi gwamnonin Arewa maso Yamma da su magance rashin tsaro ta hanyar inganta ilimi da ababen more rayuwa
  • Kungiyar ta ce saka hannun jari a fannin ilimi, noma, da walwalar jama’a na taimakawa wajen magance matsalar rashin tsaro
  • Dakta Sani Abdullahi Shinkafi, shugaban PAPSD ya ba da shawarar a yanke hukuncin kisa ga 'yan fashi da masu aikata ta'addanci a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Kungiyar PAPSD ta bukaci gwamnonin shiyyar Arewa maso Yamma da su kara habaka ci gaba a yankin ta hanyar ilimi, samar da arziki, da ababen more rayuwa.

Shugaban kungiyar Dakta Sani Abdullahi Shinkafi ne ya yi wannan kiran inda ya bayyana matsalar cin hanci da rashawa, fatara da jahilci a matsayin tushen rashin tsaro a yankin.

Dakta Sani Abdullahi Shinkafi ya yi magana kan rashin tsaro a Arewa
Dakta Shinkafi ya nemi gwamnonin Arewa maso Yamma su magance matsalar rashin tsaro. Hoto: @dikko_radda Asali: Twitter

Jaridar The Cable ta ruwaito Dakta Shinkafi ya nemi gwamnonin da su daina wahalar da kansu da kashe kudi wajen shirya tarukan zaman lafiya da tsaro a ciki da wajen Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ya jawo rashin tsaron Arewa

A cewar Dakta Shinkafi, cin hanci da rashawa, talauci, da jahilci sune manyan abubuwan da ke kyankyasar da ‘yan fashi da makami da masu aikata laifuffuka da suka addabi yankin.

Ya kuma jaddada cewa shugabannin yankin sun kasa saka hannun jari a fannin ilimi, noma, da walwalar jama’a, lamarin da ya janyo rashin tsaro a halin yanzu.

Dakta Shinkafi ya ce:

“Jahilci na daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da ‘yan fashi da kuma laifukan da suka danganci hakan, yawancin ‘yan fashin ba su da ilimin zamani da na addini.
"Shugabannin shiyyar sun kasa saka hannun jari a fannin ilimi, gina makarantun firamare da sakandare, karatun yaki da jahilci da makarantun allo”.

Dakta Shinkafi ya ba da mafita kan tsaro

Kungiyar PAPSD ta bayyana saka hannun jari a fannin ilimi, noma, da abubuwan more rayuwa a matsayin hanyar magance matsalar rashin tsaro da yankin ke fama da shi.

Dokta Shinkafi ya yi kira da a dauki matakai biyu; na amfani da makamai da kuma dabarun da ba na makamai ba a wajen yaki da rashin tsaro, inji rahoton Independent.

Ya bukaci gwamnoni da su yi amfani da jami’an soji, su amince da 'yan sandan jihohi yayin da a hannu daya kuma ya nemi a yanke hukuncin kisa ga 'yan ta'adda.

Gwamnoni sun tsara hanyar gyara tsaro

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnonin Arewa maso Yamma sun amince da wani tsari da wa'adi na kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi shiyyar.

Shugaban ƙungiyar gwamnonin shiyyar, Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana hakan a karshen taron tsaro da zaman lafiya na shiyyar da ya gudana a Katsina.

Asali: Legit.ng

People are also reading