Home Back

ZANGA-ZANGAR TSADAR RAYUWA: Yadda Ƙungiyar Ƙwadago ta tsayar da harkoki cak a Ado Ekiti

premiumtimesng.com 2024/4/28
ZANGA-ZANGAR TSADAR RAYUWA: Yadda Ƙungiyar Ƙwadago ta tsayar da harkoki cak a Ado Ekiti

Harkoki sun tsaya cankak a Ado Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, yayin da Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa reshen jihar ta amsa kiran fita zanga-zangar nuna rashin jin daɗin raɗaɗin tsadar rayuwa da ake fuskanta a faɗin ƙasar nan.

Ma’aikata sun fita zanga-zanga a ƙarƙashin Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago na jihar, Kolapo Olatunde, inda suka hallara a yankin Fajuyo.

Daga nan suka fara dagula zirga-zirgar motoci masu shiga cikin Ado Ekiri daga garin Iworoko, sai kuma masu shigowa daga tsohon titin Iyin, har ma da masu ƙoƙarin shiga Gidan Gwamnatin Jihar Ekiti da Ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha, da wasu wurare da dama.

Daga cikin kwalaye masu ɗauke da rubuce-rubuce da masu zanga-zangar su ka riƙa ɗagawa, akwai masu ɗauke da rubuce-rubuce kamar haka: ‘A gyara matatun mai’, ‘Yan Najeriya na cikin wahala’, ‘Wannan wahala ta ishe mu haka nan’, ‘A rage farashin siminti’, ‘A daina dunbuza wa ‘yan siyasa maƙudan kuɗaɗe’, da sauran su.

Yayin da ya ke wa dandazon masu zanga-zanga jawabi, Olatundecya ce Gwamnatin Tarayya ba ta da gaskiya, kuma ba ta faɗin gaskiya, musamman dangane da yadda ake tafiyar da wannan gwamnati da kuma rashin kula da jin daɗin ma’aikata a faɗin ƙasar nan.

Shugaban ma ‘yan ƙwadago ya gargaɗi gwamnati cewa ta yi fatali da shawarwarin Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF) da kuma Bankin Duniya.

Ya ce ba su da wasu shawarwari na kwarai, in banda ingiza mai kantu ruwa da su ke yi wa gwamnatin Najeriya.

“Ba da gaske su ke ba kan makomar ma’aikatan Najeriya. Mu na kira ga Gwamnatin Tarayya cewa kafin ƙarshen watan Maris ne fa wa’adin Naira 30,000 na mafi ƙanƙantar albashi ke ƙarewa.”

Ya ce gwamnati ta zo da N30,000, amma ta biya sau ɗaya.

 
People are also reading