Home Back

Rikicin Makiyaya Da Manoma Ya Salwantar Da Rayuka 6 A Taraba

leadership.ng 2024/7/2
Rikicin Makiyaya Da Manoma Ya Salwantar Da Rayuka 6 A Taraba

Mutane 6 da suka haɗa da wani dattijo mai shekaru 92 ya mutu, wasu da dama kuma suka jikkata, lokacin da wasu da ake zargin makiyaya ne suka kai hari a unguwar Mararaban Azagwa da ke ƙaramar hukumar Bali ta jihar Taraba a ranar Lahadin da ta gabata.

Rikicin ya samo asali ne bayan da aka tsinci gawar wani tsohon Bafulatani da rahotanni suka ce ya bugu da kayan maye a kasuwar Maihura. ‘Yan uwansa sun zargi mutanen kauyen Tiv da haddasa mutuwarsa, lamarin da ya kai ga harin ramuwar gayya.

Malam Isah Abdul, wani mazaunin garin ya bayyana cewa ‘yan uwan Bafulatanin da ya mutu, ba tare da wata kwakkwarar hujja ba, sun zargi mutanen kauyen Tiv tare da far musu.

Shugaban Majalisar Gargajiya ta Tiv a Jihar Taraba, Zaki David Gbaa, ya tabbatar da mutuwar, sannan ya bayyana sunayen waɗanda suka mutun a matsayin Aondohemba Salemkaan, da Tersuugh Dondo, da Terkuma Mbatim, da Kumaga Ujam Asaaga Nev, da kuma Tersoo Memga.

Gbaa ya yi Allah-wadai da harin, amma ya yaba wa jami’an tsaro da suka yi gaggawar mayar da martani, yana mai fatan ganin an kama wadanda suka kai harin tare da hukunta su.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, DSP Gambo Kwache, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma bayyana cewa ‘yansandan sun gano gawarwaki biyu kacal.

Ya ƙara da cewa har yanzu ba a kama wani mutum ba, amma jami’an tsaro na ci gaba da bincike a yankin domin gano maharan.

People are also reading