Jigo a APC Ya Wanke Tinubu Daga Zargi Kan Wuyar da Ake Sha a Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Jigo a jam'iyyar APC, Ismaeel Ahmed, ya wanke shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan taɓarɓarewar da tattalin arziƙin ƙasar nan ya yi.
Ismaeel ya bayyana cewa bai kamata a ɗora alhakin halin da ƙasar nan ke ciki ba a kan shugaban ƙasar duk da yanayin tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki da ƴan Najeriya ke fama da su.
Ismaeel Ahmed ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na 'Politics Today' ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa matakai masu tsauri da gwamnati mai ci ta ɗauka sun zama wajibi ne domin farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan.
"An ɗauki tsauraran matakai. Babu ɗaya daga cikin waɗannan matakan da ba a yi alƙawari ba a lokacin yakin neman zaɓe ba, ba wai shugaban ƙasa Bola Tinubu kaɗai ba, har ma da sauran ƴan takara."
"Muna cikin wani yanayi da ya kamata al’amura su daidaita. Shugaban ƙasa ya ɗauki tsauraran matakai, abin ba daɗi, dukkanmu muna ji a jikinmu, amma ba zan ce shugaban ƙasa za a ɗorawa laifi ba."
- Ismaeel Ahmed
Jigon na APC ya ce kafin zaɓen shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, ƴan takarar jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi da takwaransa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar sun yi alƙawarin kawo ƙarshen tallafin man fetur.
'Yan APC sun fadi wadanda suka sanya su yin zanga-zangar adawa da Ganduje
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta ɗora alhakin halin matsin tattalin arziƙin da ake fama da shi a ƙasar nan kan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Ƙungiyar ta bayyana cewa wasu daga cikin manufofin da gwamnatin Tinubu ta kawo ne silar jefa ƴan Najeriya cikin halin wuya a ƙasar nan.
Asali: Legit.ng