Home Back

Kashim Shettima Ya Mayar Da Martani Kan Tsadar Rayuwa

leadership.ng 2024/4/28
Kashim Shettima Ya Mayar Da Martani Kan Tsadar Rayuwa

Fadar Shugaban Kasar ta yi Allah wadai da shekaru da dama da aka shafe ana tafka ta’asa da rashin amfani da kadarorin kasar a ciki da wajen iyakokin kasar, lamarin da ke janyo asarar kudaden shiga da ke kawo cikas ga ci gaban tattalin arziki.

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ne ya bayyana hakan jiya a wajen taron kula da dukiyar al’umma a Abuja.

Shettima ya ce an kama manyan motoci 45 dauke da masara a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa kasashen makwabta da tsakar daren ranar Lahadi.

Ya ce, “A cikin dare uku da suka wuce, an kama manyan motoci 45 na masara ana jigilar su zuwa kasashe makwabta. Kawai a cikin Kauyen Ilela, akwai hanyoyin fasa kwauri guda 32. Kuma a lokacin da aka kama wadannan kayan abinci, farashin masara ya fadi da Naira 10,000. Wato ana sayar da ita Naira Naira 60,000 ta sakko zuwa Naira 50,000.

“Don haka, akwai wadanda ke da aniyar yi wa al’ummarmu zagon kasa, amma wannan lokaci ne da ya kamata mu hada kai zuwa wata kungiya mai zaman kanta. Dole ne mu tsaya mu yi wa kasa aiki. A yanzu mun wuce batun siyasa, magana ake ta a tsaya a fuskanci gwamnati.

“Abin takaicin shi ne, har yanzu wasu daga cikin ‘yan kasarmu sun tsunduma a cikin salon siyasa. Su ne masu aikata ta’addanci, suna ba da shawarar cewa Najeriya ta bi irin hanyar da Lebanon ke kai. Amma hakan ba za ta yiwu ba, domin Nijeriya ta fi karfin haka, kuma da sannu za a shawo kan lamarin.”

A cewar Shettima, maimakon su jira har zuwa 2027, ‘yan siyasa masu ra’ayin rikau wadanda ba za su iya samun madafun iko ta hanyar katin zabe ba, sun gwammace su jefa kasar nan cikin halin rashin tabbas.

Mataimakin shugaban kasar ya amince cewa ‘yan Nijeriya na fuskantar kalubale, ya kuma bukaci a yi hakuri, domin ya bayyana kwarin gwiwar cewa nan ba da dadewa ba al’amura za su canja.

Shettima, who represented Tinubu at the ebent, hinted at plans by the present administration to create millions of jobs by unlocking the balue of Nigeria’s bast public assets to optimize and double the country’s Gross Domestic Product (GDP).

Shettima, wanda ya wakilci Tinubu a wajen taron, ya yi ishara da tsare-tsare da gwamnati mai ci ke yi na samar da miliyoyin ayyukan yi ta hanyar bude dimbin kadarorin al’ummar Nijeriya don ingantawa tare da ninka arzikin kasa (GDP).

Ya ce tare da farfado da tattalin arziki a matsayin babban abin da ta sa a gaba, gwamnatin tarayya na da burin tara akalla Dala biliyan 10 domin kara kudin musayar kudaden waje wanda hakan kuma zai daidaita darajar Naira.

Ministan kudin ya ba da tabbacin cewa yayin da ake sakin ton 42,000 na hatsi iri-iri tare da ton 60,000 nan gaba kadan, a wani mataki na dakile hauhawar farashin kayan abinci, farashin kayan abinci zai ragu a watanni masu zuwa sakamakon ayyuka da manufofin gwamnati.

An shirya taron ne domin tsara dabarun sarrafa dukiyoyi da albarkatun kasa yadda ya kamata domin inganta jin dadin al’ummarta.

 
People are also reading