Home Back

Shin ko dabanci na son dawowa ne a birnin Kano?

bbc.com 2024/7/5
..

Asalin hoton, NPF

Batun dabanci shi ne ke kankane hira a majalisu da tattaunawa a kafafen watsa labarai na birnin Kano, a ƴan kwanakin nan sakamakon kome da ayyukan ƴan daba suka yi a birnin, bayan magance matsalar da gwamnatoci suka yi a baya.

Mutane da dama na barin wasu unguwannin birnin a yanzu haka saboda yanayin rashin tsaro sannan mutanen da ke zaune a unguwannin kuma suna cikin fargaba.

Rahotanni na cewa al'ummar jihohi maƙwabta da ke shiga Kano domin kasuwanci na ƙaurace wa birnin saboda rashin tabbas na abin da zai je ya zo idan suka shiga Kanon.

Girmar matsalar ta fito fili a unguwar Ja'en inda rikici ya ɓarke tsakanin ƴan sintiri da ƴan dabar al'amarin da ya yi sanadiyyar mutuwar shugaban 'yan sintirin yankin.

Al'amarin ya kai ga tilasta sabon kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Salman Dogo Garba ya lashi takobin saka ƙafar wando ɗaya da harkar dabanci.

Abin tambaya a nan shi ne me ke janyo dabanci a Kano? Ko dabancin ya yi kome ne a birnin?

Me ke janyo ayyukan daba?

Masana halayyar ɗan adam da zamantakewa na danganta dabanci da abubuwa kamar haka:

  • Lalacewar tarbiyya
  • Rashin kula daga iyaye
  • Shaye-shaye
  • Jahilci
  • Talauci
  • Rashin shugabanci na gari

"Siyasa ce ta sa aka kasa magance daba a Kano"

Malam Kabiru Dakata wanda mai sharhi ne kan al'amuran yau da kullum a Kano ya ce shi a ganinsa "siyasa" ce ta hana a magance matsalar dabanci a Kano.

"Idan za a iya tunawa a shekarun baya an samu rabuwar kai tsakanin 'yan siyasa jihar Kano , abin da ya kai ga wasu sun kafa nasu tsagin da ake kira G7, a junansu suka rinka ƙalubalantar junansu, da amfani da ƴan daba wajen ƙone-ƙone da sare-saren jama'a a ofisoshin tsagin. Kuma irin wannan abun haka ya ci gaba har a zaɓen 2023.

Abu na biyu lokacin da hukumar 'yansanda ke iya ƙoƙarinta ƙarƙashi sashenta na yaƙi da daba wato "anti-daba" domin kakkaɓe irin waɗannan migayun dabi'u sai rikicin masarauta ya kunno kai.

Don haka an wayi gari hankalin hukumar 'yan sandan Kano ya fi karfi wajen kare gidan Nasarawa inda Aminu Ado Bayero ke zama da kuma Kofar kudu inda Muhammadu Sanusi II ke zama." In ji Kabiru Dakata.

Kabiru Dakata ya ƙara da cewa "tarin 'yan sanda da aka jibge a wadannan wurare biyu ba ƙaramin kassara ayyukan tsaron Kano suka yi ba, domin 'yan sandan da ya kamata a ce sun kare rayukan dubban mutane an tattara ga wasu mutane kalilan.

Idan da a ce 'yansandan an tattara su zuwa unguwanni da ake samun waɗannan matsaloli da an samu sauki. Wannan ya bai wa 'yan daba damar cin karensu babu babbaka. Kuma babu mai sa musu ido ko hana su komai yanzu haka a Kano."

Abu na uku a cewar Kabiru Dakata shi ne "al'umma, domin akwai bukatar hadin-kai tsakanin al'umma da jami'an tsaro wajen kawo karshen daba. Sai dai akwai tsoro a zukatan mutane wasu kuma na ganin suna da alaƙa ta jini ko sanayya da 'yan dabar don haka ba sa kai ƙorafi ko tuntuɓar jami'an tsaro da ba su wasu bayanan.

Abu na karshe shi ne matsalar rashin aikinyi da ta yi wa matsa katutu da kuma shaye-shaye da ke ingiza matasa cikin harkar daba." in ji Malam Kabiru Dakata.

Hanyoyin magance dabanci a Kano

Kabiru Dakata ya kuma lissafa wasu hanyoyi guda biyar da ya ce su ne kawai za su magance matsalar dabanci a birnin nan Kano:

Haɗin kan al'umma: Wajibi al'umma a ungwanni su haɗe kansu wajen tabbatar da cewa duk mutumin da ke wannan aiki na daba sun kai sunan shi wajen jami'an tsaro kuma idan an kama su za su bayar da goyon baya.

Tattaunawa da Matasa: Sanna akwai buƙatar zama da matasa a unguwa a taimaka musu ta harkar ilimi da sana'oi da dai sauransu. Don haka akwai rawar da al'umma a matakin unguwa za su taka matuka wajen kawo sauki.

Daina sakin masu laifi: Sannan a mafi yawanc lokuta idan an kama 'yan daba ana samu mutane masu kumbar susa da ke sakin su. Don haka dole 'yan sanda su tashi tsaye wajen dagewa da rashin bada irin wannan kofa da gudanar da aiki bisa ka'ida da ƙwarewa.

Shugabanni su ji tsoron Allah: Abin takaici ne ka ga dan siyasa ya killace 'ya'yansa wasu ma an kai su ketare karatu amma 'ya'yan talakawa ana ingiza su ana amfani da su wajen daba domin cimma muradai na kashin kai musamman lokacin kamfe. Saboda haka dole ne ƴan siyasa su ji tsoron Allah su guji amfani da ƴaƴan mutane domin biyan buƙatun kansu.

Jagoranci na gari: Dole ne gwamnatoci su tabbatar da sun yi jagoranci na gari ta hanyar kyautata wa al'ummar da suka zaɓe su ta fuskar bai wa matasa aikin yi da ilimi domin samun makoma mai kyau.

Me ƴansanda ke yi?

A tattaunawarsa da BBC, kakakin 'yansanda jihar Kano SP Abdullahi Kiyawa ya ce tabbas sun yi fama da wannan matsala amma kawo sabon kwamishinan 'yansanda ya sa an soma ganin sauki.

SP Kiyawa ya ce dama unguwanni da wannan matsala ta addaba a kwaryar birnin Kano su ne Dala, Dorayi da Ja'en, kuma tuni suka murkushe 'yan daban tare da kama mutane 16.

"Kwashina ya kai ziyarar gani da ido a ranar 26 ga watan Yuni inda ya gana da al'umma yakin kan neman hadin-kai kawo karshen matsalar. Ya ce an kashe mutane a Dala da Ja'en kuma ya je ya yi wa iyalansu ta'azziya.

Sannan ya bijiro da wasu matakai na hada kan jami'an tsaro da ganawa da masu ruwa da tsaki da karfafa ayyukan sintiri, sannan ya kawo dabarun ayyuka da naurorin zamani da bincike. Sannan duk mutanen da aka kama an kai su sashin binciken manyan laifuka domin fuskantar shari'a". In ji SP Kiyawa.

SP Kiyawa ya kuma ce sakin 'yandaba kamar yadda ake zargi ba laifinsu ba ne, kotu ake gurfanar da su don haka wani abu idan ya biyo baya ba daga su ba ne. Sai dai kuma ya ƙara da cewa suna nazari domin ganin yadda za a yi wa tufkar hanci.

To amma mai magnaa da yawun rundunar 'yan sandan na Kano ya ƙi ya ce uffan dangane da zargin cewa 'yan siyasa ne ke marawa ayyukan daba baya, amma za su tsaya tsayin daka wajen shawo kan matsalar.

Jami'in ya ce aikin ba na mutum guda ba ne shi ya sa suke neman taimako da ankarar da al'umma a kodayaushe wajen ganin sauki ya samu.

People are also reading