Home Back

Jihar Yobe Ta Kashe Naira Miliyan ₦179 Wajen Tallafawa Mahajjata 1,332

leadership.ng 2024/7/3
Jihar Yobe Ta Kashe Naira Miliyan ₦179 Wajen Tallafawa Mahajjata 1,332

Hukumar Alhazai ta jihar Yobe ta bayar da tallafin Naira miliyan 179.8 ga maniyyata 1,332 don gudanar da aikin Hajjin shekarar 2024, kamar yadda babban daraktan yaɗa labarai da Mamman Mohammed ya sanar wa Gwamna Mai Mala Buni.

Kowane mahajjaci ya samu tallafin ₦135,000 (BTA). Shugaban hukumar Alhaji Mai Aliyu ya bayyanawa gwamnan kan nasarar jigilar dukkan maniyyata da jami’ai zuwa ƙasar Saudiyya, inda tuni suka fara gudanar da ayyukan ibada a Madina da Makkah.

Hukumar ta samar da masaukin Otal a tsakanin tazarar tafiya da masallatai masu tsarki, tare da tabbatar da dacewa da jin dadin mahajjata.

Alhaji Mai Aliyu ya shaida cewa dukkan maniyyatan suna cikin koshin lafiya, kuma ya yi addu’ar Allah ya ƙarawa jihar da ƙasa zaman lafiya.

Gwamna Buni ya yabawa hukumar da kamfanonin jiragen sama kan yadda ake jigilar maniyyata a kan lokaci tare da jaddada muhimmancin ba da fifiko ga jin daɗinsu.

Gwamna Buni ya bukaci hukumar da ta ci gaba da yi wa alhazai hidima yadda ya kamata, ya kuma tunatar da maniyyatan da su gudanar da rayuwarsu cikin lumana kamar yadda al’adar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya koyar. Ya kuma yi addu’ar Allah ya karɓa musu ibadun su ya kuma mayar da su gida lafiya.

People are also reading