Sojojin Najeriya Sun Hallaka Ƴan Bindiga Sama da 100 Ana Shagalin Sallah a Arewa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina - Rundunar sojin saman Najeriya ta kashe ƴan bindiga sama da 100 a wani samame da ta kai sansanin Kuka Shidda da ke karamar hukumar Faskari a jihar Katsina.
Dakarun sojojin rundunar Operation Hadarin Daji ne suka yi ruwan wuta kan ƴan bindigar da daddare, wanda bisa nasara suka murgushe su da yawa a yankin Faskari.
Sojojin sun kai samamen ne a sansanin kasurgumin ɗan bindiga, Yusuf Yellowa da babban yaronsa Rabe Imani, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Kaula ya fitar, ya ce sama da babura 45 aka lalata a yayin harin da jiragen sojojin suka kai.
Ya ce wannan shi ne karo na uku da sojojin saman Najeriya suka samu nasarar kai farmaki da kashe ƴan ta'adda a yankin Faskari-Kankara kwanan nan.
Kaura da ƙara da cewa jami'an tsaro sun samu nasarar daƙile yunkurin garkuwa da mutane da safiyar ranar Lahadi a yankin ƙaramar hukumar Jibia.
"Ƴan sanda sun samu kiran gaggawa kan wani harin garkuwa da mutane da aka kai yankin Kwata a ƙaramar hukumar Jibia da misalin karfe 4:15 na asuba.
"Nan take suka kai ɗauke, suka tare hanyar da ƴan bindigar za su wuce, aka yi musayar wuta wanda daga ƙarshe maharan suka arce suka bar mata 3 da suka ɗauƙo," in ji shi.
Ya ce dakarun ƴan sandan sun ceto Ummulkhari Abubakar (23) Shafa’atu Abubakar (35), da kuma Maryam Lawal (15) cikin ƙoshin lafiya.
A wani rahoton kun ji cewa Sojojin saman Najeriya sun mayar da martani, sun kashe tulin ƴan bindiga a jihar Katsina bayan harin da aka kai yankin Ƙankara.
Sakataren watsa labaran gwamna, Ibrahim Kaula ya ce rahoton bayan samamen sojin ya nuna ƴan bindiga 29 sun bakunci lahira.
Asali: Legit.ng