Home Back

Sojojin Najeriya Sun Hallaka Ƴan Bindiga Sama da 100 Ana Shagalin Sallah a Arewa

legit.ng 2024/6/29
  • Jirgin yaƙi ya kai samame sansanin ƴan bindiga, ya yi nasarar hallaka aƙalla ƴan ta'adda 100 a yankin ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina
  • Mai magana da yawun gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Kaula ya ce sojojin sun lalata babura sama da 45 da wasu kayan aikin ƴan bindigar
  • Kaula ya bayyana cewa dakarun ƴan sanda sun yi nasarar daƙile harin garkuwa da mutane tare da ceto mata uku a Jibia

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina - Rundunar sojin saman Najeriya ta kashe ƴan bindiga sama da 100 a wani samame da ta kai sansanin Kuka Shidda da ke karamar hukumar Faskari a jihar Katsina.

Dakarun sojojin rundunar Operation Hadarin Daji ne suka yi ruwan wuta kan ƴan bindigar da daddare, wanda bisa nasara suka murgushe su da yawa a yankin Faskari.

Jirgin sojojin saman Najeriya.
Jirgin yaƙi ya ragargaji ƴan bindiga a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina Hoto: Nigeria Air Force Asali: Facebook

Sojojin sun kai samamen ne a sansanin kasurgumin ɗan bindiga, Yusuf Yellowa da babban yaronsa Rabe Imani, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Kaula ya fitar, ya ce sama da babura 45 aka lalata a yayin harin da jiragen sojojin suka kai.

Ya ce wannan shi ne karo na uku da sojojin saman Najeriya suka samu nasarar kai farmaki da kashe ƴan ta'adda a yankin Faskari-Kankara kwanan nan.

Kaura da ƙara da cewa jami'an tsaro sun samu nasarar daƙile yunkurin garkuwa da mutane da safiyar ranar Lahadi a yankin ƙaramar hukumar Jibia.

"Ƴan sanda sun samu kiran gaggawa kan wani harin garkuwa da mutane da aka kai yankin Kwata a ƙaramar hukumar Jibia da misalin karfe 4:15 na asuba.
"Nan take suka kai ɗauke, suka tare hanyar da ƴan bindigar za su wuce, aka yi musayar wuta wanda daga ƙarshe maharan suka arce suka bar mata 3 da suka ɗauƙo," in ji shi.

Ya ce dakarun ƴan sandan sun ceto Ummulkhari Abubakar (23) Shafa’atu Abubakar (35), da kuma Maryam Lawal (15) cikin ƙoshin lafiya.

Jigirin yaƙi ya samu nasara a Bakori

A wani rahoton kun ji cewa Sojojin saman Najeriya sun mayar da martani, sun kashe tulin ƴan bindiga a jihar Katsina bayan harin da aka kai yankin Ƙankara.

Sakataren watsa labaran gwamna, Ibrahim Kaula ya ce rahoton bayan samamen sojin ya nuna ƴan bindiga 29 sun bakunci lahira.

Asali: Legit.ng

People are also reading