Tsadar Rayuwa: Gwamnan Arewa Ya Yi Abu 1 da Ya Faranta Ran Ma’aikatan Jiharsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Jigawa - Gwamnatin jihar Jigawa ta ware Naira biliyan 1.1 domi siyan karin kayan abinci na gaggawa da za a sayarwa ma'aikatan jihar.
Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu, Sagir Musa ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a jiya Alhamis.
Sagir Musa ya ce gwamnati ta cimma wannan matsayar ne a taron majalisar zartarwa da ya gudana a ranar Litinin da nufin saukakawa ma'aikatan kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kayayyakin da za a siya sun hada da buhunan shinkafa 12,000 da katon 15,000 na taliya, wanda za a sayarwa ma’aikatan gwamnatin kan farashi mai rahusa.
Ya ce siyan kayan abincin na cikin shirin gwamnatin jihar na samar da shaguna na hadin gwiwa a dukkan kananan hukumomi 27 na jihar.
Jaridar Leadership ta rahoto kwamishinan na nuni da cewa za ayi amfani da shagunan a matsayin wuraren da ma'aikatan jihar za su rika sayen kayan abinci a farashi mai rahusa.
Sagiru ya ce tuni aka samar da hanyoyin kafawa da sarrafa shagunan hadin gwiwar inda ma’aikata za su iya karbar kayan abinci a kan bashi da kuma biyan kudin kadan-kadan.
Kwamishinan ya kara da cewa an kashe N2.8bn a shirin ciyar da al'uma abinci a watan Ramadan na bana.
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnatin jihar Jigawa ta yi karin albashi na Naira 30,000 ga ma'aikatan jihar wanda zai yi aiki na watanni uku.
A cewar gwamnatin jihar, an yi karin albashin ne domin rage wa ma'aikatan radadin tsadar rayuwa da kasar ke fuskanta sakamakon janye tallafin man fetur.
Asali: Legit.ng